Connect with us

KASUWANCI

Majalisar Dattawa Ta Dora Wa Kwamitinta Nauyin Tantance Emefiele

Published

on

A Ranar Talatar data gabata, Majalisar Dattawa ta dorawa kwamitinta na Banki da Inshora da kuma sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su tantance Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele.

An baiwa kwamtin waadin sati daya ya kammala tantance Mista Godwin Emefiele ya kuma gabatarwa da Majalisar rahoton sa na tantancewar yadda Majalisar zata dauki matakan da suka dace.

In ba’ manta ba, a satin da ya gabata ne Mista Godwin Emefiele Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara amincewa Gwamnan wa’adi na biyu na shugabancin Babban Bankin na CBN na tsawon wa’adin shekaru biyar.

Har ila yau, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Majalisar ta Dattawa su amince da sabon wa’adin na Mista Godwin Emefiele.

A karamin zaman da Majalisar Dattawan ta yi a ranar Talatar data gaba, Shugaban masu tinjaye na Majalisar ta Dattawa Sanata Ahmad Lawan dan jamiyyar APC daga jihar Yobe ga gabatar da a amince da sabon wa’adin na Mista Godwin Emefiele kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Har ila yau Mataimakin Marasa rinjaye na Majalisar ta Dattawa Sanata Philip Aduda dan jamiyyar PDP da ya fito daga babban birnin tarayyat Abuja ya goyi bayan kudurin na.

Shugaban Majalisar ta Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya amince zabo Mista Godwin, inda ya umarci kwamitin banki da Inshora da kuma saura cibiyoyin hada-hadar kudi su tantance Gwamnan na Babban Bankin Nijeriya Mista Godwin su kuma gabatarwa da Majalisar rahoton su a cikin sati daya.

Mista Godwin ana sa ran zai kammala wa’adin sa na farko na shugabancin Babban Bankin na Nijeriya CBN a ranar biyu ga watan Yuni ganin cewar, an nada shi gwamnan bankin a ranar biyun ga watan Yunin shekarar 2014 da tsohon Shugaban kasa Mista Goodluck Jonathan ya yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!