Connect with us

RAHOTANNI

Osibanjo Ya Kaddamar Da Shirin Inshorar Kiwon Lafiya Na Jihar Bauchi

Published

on

Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Profesa Yemi Osibanjo ya kaddamar da shirin inshorar kiwon lafiya na Jihar Bauchi. Shirin wanda aka kaddamar ranar asabat da ta gabata ya samu halartar gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar da mataimakin shugaban kasa Profesa Yemi Osibanjo da wasu ministoci, inda kafin kaddamar da wannan shirin sai da ya je garin Burra a karamar hukumar Ningi ya kaddamar da aikin wutar lantarki da wasu ayyuka da gwamnati ta samar.

Cikin jawabinsa mataimakin shugaban kasa Osibanjo ya yaba da kaddamar da shirin wanda ya ce zai taimaki masu karamin karfi. Don haka ya bayyana akwai bukatar dukkan jihohin kasar nan su kaddamar da irin wannan shiri. Kuma gwamnatin tarayya za ta fadada shirin inshora na kasa don kowa ya samu shiga cikin shirin a samu ingantuwar kiwon lafiya a Nijeriya.

Dokta masur Dada shine shugaban hukumar lura da inshorar lafiya na Jihar Bauchi ya bayyana cewa an kaddamar da shirye shiryen guda biyu masu muhimmanci don tallafawa jama’a musamman talakawa don a taimaka wajen samun saukin jinya da kare mutum daga kamuwa da cututtuka don rayuwa ta inganta. Ya ce shirin Health contributory scheme shiri ne da mutane za su rika sanya kudi kashi goma cikin dari don cin gajiyar shirin ma’aikaci ko dan kasuwa.

Dokta Mansur Dada ya kara da cewa shirin zai taimaka sosai saboda idan jinya ta samu mutum ko iyalinsa a lokacin da ba shi da kudi zai kasance ya je asibiti likita ya duba shi an bashi magani kusan kyauta saboda gwamnati za ta biya kashi cas’in shi ya biya kashi goma cikin dari. Kuma shirin zai rika taimakon mutane milyan bakwai na jihar

Bauchi, don haka kowa zai iya shiga ba sai ma’aikacin gwamnati ba.

Amma marasa galihu da musakai gwamnati ne za ta rika biya musu don a duba lafiyar su kyauta a karkashin wannan hukuma. Dokta Aminu Magashi Garba shine shugaban kungiyar Africa Health Budget network wato kungiya mai nazarin kasafin kudin da gwamnatoci ke warewa kan kiwon lafiya a kasashen Africa. Inda cikin jawabin sa ya bayyana cewa sun jima suna bin gwamnatocin jihohi da shugabannin kasashen Africa don ganin an tabbatar da samar da kason kudin kiwon lafiya an tabbatar da yin aiki da shi kamar yadda aka tanada.

Inda Dokta Aminu Magashi ya kara da cewa sun sha zuwa Jihar Bauchi don bin kundin neman ganin an kirkiro wadannan hukumomi har zuwa wannan lokaci da aka kai ga nasara mataimakin shugaban kasa Osibanjo ya kaddamar da shirin. Don haka ya bayyana cewa sun je majalisun jihohi da na tarayya a jihohi da kasashe don ganin yadda mutane za su samu sauki wajen lura da lafiyar su idan sun shiga cikin wannan shiri na kiwon lafiya ta hanyar amfani da inshorar kiwon lafiya a kowace jiha ko kasa. Ya kara da cewa shirin zai amfani duk mai bukata ko da ba ma’aikaci ba ne zai iya shiga cikin shirin don ya amfana da shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!