Connect with us

LABARAI

Rashin Sinadari Ne Dalilin Jinkirta Fara Sarrafa Biredin Rogo –Audu Ogbeh

Published

on

­Ministan ayyukan gona da ci gaban karkara, Audu Ogbeh ya bayyana cewa rashin wasu sinadarai da ake amfani da su wajen sarrafa rogo don yin biredi ne ya jawo aka jinkirta fara sarrafa rogon don yin biredi.

Sinadarin mai suna “Sure-bake Yeast” wanda ake amfani da shi wajen sarrafa biredi mai matukar inganci, sannan ya na kara saukaka sarrafa rogon don yin biredi da shi.

Ministan ya bayyana cewa ana gab da shawo kan wannan matsala, saboda Nijeriya za ta hada gwiwa da kasar Amurka don samar da wannan sinadarin, ta hanyar samar da shi a nan gida Nijeriya.

Ministan ya bayyana cewa akwai kamfanoni masu zaman kansu da su ma suke sha’awar samar da wannan sinadarin tare da hadin gwiwar gwamnatin, ministan ya bayyana cewa gwamnati na neman hadin gwiwar babban bankin Nijeriya da wasu kamfanonin noma don cimma wannan muradin
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!