Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Swaziland Ya Kafa Dokar Kowa Ya Auri Mata Biyar Ko A Daure Shi

Published

on

Basaraken kasar Swaziland, King Mswati III, ya shelanta sabuwar doka ga ‘yan kasar wacce ke cewa daga watan Yuni, 2019, ana bukatar duk wani baligin namiji dan asalin kasar da ya tabbatar da ya auri akalla matan aure biyar, ko kuma a garkame shi a gidan Yari.

Cikin wata sanarwa, Sarkin ya yi kira ga dukkanin mazajen kasar da su auri akalla mata biyar kowannen su, yana kuma mai ba su tabbaci da cewa, gwamnati ce za ta biya dukkanin kudaden shagulgulan auren na su, gwamnatin kasar kuma za ta saya masu gidajen zama da matayen na su.

“Ga yanda dokar take, ka auri akalla mata biyar, kana da tabbacin gwamnati za ta biya maka duk kudaden shagulgulan auren na su, za kuma ta saya maka gidajen da za ka ajiye matan naka.”

Wani Mutum a kasar Swaziland da matayen aurensa hudu

King Mswati, ya hada da gargadin cewa, duk wani mutum namiji ko mace da suka kalubalanci wannan sabuwar dokar za su fuskanci daurin rai-da-rai a gidan Yari.

Dokar a cewar IHarare, an kafa ta ne domin tabbatar da ganin kowace mace ta sami mijin aure a cikin kasar, kamar yanda masu kafa dokar ke ganin matukar dai mazaje suka rika auran akalla mata biyar hakan zai taimaka wajen ganin kowace mace ta sami mijin aure.

Basaraken, ya yi nuni da cewa, mata sun fi maza yawa nesa ba kusa ba a kasar ta Swaziland, wanda ya yi nuni da cewa, hakan kuwa babbar matsala ce ga kasar wacce ta shahara cike da ‘yan mata budurwowi.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, gwamnatin kasar ta kafa dokar ce a kan yanda ‘yan mata suke ta kara yawaita da kuma karantar mazaje a cikin kasar ta Swaziland.

Shi a kankin kansa, Sarki Mswati, matan aure 15 yake zaune tare da su, da kuma ‘ya’ya 25, sa’ilin da mahaifinsa wanda ya gada yake da sama da matan aure 70 da kuma ‘ya’ya 150.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!