Connect with us

MAKALAR YAU

Wadanda Suka Hana Kwankwaso Zuwa Kano Ne Su Suka Sa Ganduje Ruguza Masarautar Kano

Published

on

A wannan lokaci babu wani batu ko magana da ake yi kamar batun da ya shafi kirkira sabbin masarautu har guda hudu a jihar Kano saboda dalilai na siyasa, wannan al’amari yana kan gaba wajan daukar hankalin mafiyawan ‘yan Najeriya tare da mabanbantar ra’ayoyi.

Wannan tasa kowa da yadda yake kallon abun, sannan kuma akwai fassara iri daban-daban daga wadanda suka san sarauta da ma wadanda ba san abinda ake kira da sarauta ba, haka dai wannan batu ke yawo musamman a kafafen sadarwa na zamani watau soshiyal midiya.

Dangane da danbarwar da ke faruwa a masarautar Kano a kullin abubuwa sai kara fitowa fili suke akan wadanda su ke da hannu wajan aikata wannan abin kunyar wanda ya zuwa yanzu lamarin yana shan soka da Allah wadai daga kowane bangare amma duk da haka sai anyi daga karshe dai muna fatan za a ga abinda ba a so.

Akan wannan batu ina da ra’ayi da mahanga guda biyu, na farko dai idan muka duba yadda wannan lamari yake tafiya za mu iya tabbatar da cewa akwai wadanda suke bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wajan aiwatar da wannan mummunan kudiri.

Na biyu kuma ina da ra’ayin cewa ana son yin amfani da wannan damar ne domin kauda hankali al’umma daga irin sakaci da bala’o’in da gwamnatin shugaban Buhari ta haifar na rashin tsaro a arewacin Najeriya saboda haka a kirkira wani abu da zai dauke hankali jama’a musamman a wannan lokacin na watan Ramadan mai falala.

Idan muka koma bayan zamu iya fahimtar cewa lokacin da tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yake cikin tsaka mai wuya akan makomar siyasar sa, ya kusa rasa inda zai sa kanshi a siyasance, kamar abin nan da bahaushe ke cewa rana zafi inuwa kona.

Sannan wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari tarihi ya nuna cewa duk mutumin da ya kuskura ya fada mata gaskiya ko Bola Ahmad Tunubu ya haifeshi sai ta ga bayansa balanta wani mutum da ake gani da kima a yanke arewa saboda haka zai gane kuskuran da ya yi komin daran dadewa.

Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sunusi ya cika tsoma bakinsa cikin abubuwan da suka shafi siyasa musamman yana ganin cewa a matsayinsa na Sarki abubuwa na tafiya ba dai dai ba saboda haka sai ya tanka.       

Tunda ya fara wancan maganar ta nunawa gwamnatin Buhari gaskiya jama’a da dama suke fara jiran wannan lokacin domin ganin yadda zata kaya, ko a wancan lokacin sai da fadar shugaban kasa tasa talakan Sarkin Kano Malam Garba Shehu ya maidawa Mai Martaba Sarki martani amma cikin kyakkyawan lafazi da girmamawa.

Duk da haka Sarki yana ganin su uwaye na al’umma saboda duk abinda ya shafi al’umma kai tsaye za su tsoma bakinsu wannan dai bata hana Mai Martaba Sarki yin magana ba da zaran ya samu da ma kuma ya ga abinda zai tanka sai ya tanka.

A iya tunanina tun a wancan lokacin suke farautarsa da wani laifi da za su yi guguwa ya Rasulu da rawaninsa kowa ya huta, duk da cewa abin yana da wahalar gaske ayi shi kai tsaye daga fadar shugaba kasa sai dai suna da baban Yaro wanda zai iya yin komi domin ya dadadawa fadar shugaban kasa.

Idan za mu tuna, an bullo da zargin cewa Mai Martaba Sarkin Kano ya yi amfani da rawaninsa wajan barnata dukiyar masarautar Kano saboda haka dole za a yi bincike domin gano gaskiyar lamari wannan fa daya ne daga cikin umarnin da manya da suka hana Kwankwaso zuwa Kano suka ba Ganduje domin dai Mai Martaba ya yi shiru da bakinsa a cigaba da yin ba dai dai ba.

A nasa bangare Mai martaba Sarki da ya lura cewa mutanen sun fi shi iya komi kuma yana karkashinsu ne, sai ya rufawa kansa asiri ya yi  shiru a wancan lokacin saboda haka sai maganar ta kwaranye, shiru kake ji kamar an aiki Bawa garinsu.

Daga nan sai a koma zaman idan ka yi mana muma za mu yi maka, lokacin da aka buga gangar siyasa, abubuwa sun jagule a jihar Kano, jiha mai mutunci, jiha Mai tarihi, jiha mai kima a idon duniya, jihar da ake koyi da ita wajan siyasa, jiha daya tamkar da goma, sai kawai hannun agogo ya dawo baya.

Irin abubuwan da suka rika faruwa abin ya kazanta wanda yasa dole sarki ya rika magana da jan hankali akan ‘yan siyasa da sauran jama’a domin dai kadda a bata tarihin jihar, wannan ya zama wani sabon babi ga Mai Martaba Sarki na ya rika tsoma baki a cikin abubuwa da suka shafi harkokin siyasa.

Kadda mu manta, bayan Kwankwaso ya samu wani yanayi mai kama da ‘yancin siyasa ya dawo Kano ya cigaba da yakin neman zabe tare da tallata ‘yan takarasa a gefe guda kuma bangaran gwamnati sun dauki zafi so sai game da kwankwaso da sauran ‘yan tafiyarsa.

A daidai wannan lokacin ana son duk wanda baya cikin sha’anin siyasa ya kama bakinsa ya yi shiru domin dai za a shirya rashin gaskiya tare da wadanda suke goyan bayan rashin gaskiya daga fadar shugaban kasa, suna kyalla idanu sai kawai suka hango Sarki Sunusi kuma suka tabbatar cewa ba zai iya yin shiru ba idan aka yi rashin gaskiya.

Fara yin nasiharsa ke da wuya sai kawai batun ya dauki wani sabon salo, sannan kuma abin ya zama biyu a gefe guda suna kallon yadda zata kaya tsakaninsu da al’umma jihar Kano da suka yi niyyar yi masu korar kare ta hanyar zaban Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP duk da cewa su Ganduje sune ke da mulki da iko wanda suka ce ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai sun koma.

A wannan iskar mai kadawa duk wanda ka ji shi yana irin wannan kalamai a yanayin siyasa da ya dauki zafi lallai yana da abinda ya dogara da shi, domin idan ba haka ba babu wani mahaluki da ya isa ya rika ambaton tsiya a jihar Kano kuma har ya yi nasara babu shi ko wanene.

Wannan shi ne kadan daga cikin abubuwan da duk wani mai bibiyar harkokin siyasar jihar Kano zai fara tunawa duk lokacin da aka tada maganar danbarwar masarautar jihar Kano idan kuma bai san wannan dan tarihi ba, yanzu zaka ji shi ya saki layi yana fangima cikin batun da bai san ta inda aka fara ba balanta inda za a kare.

Karin wasu masarauta da aka yi kadan ne daga cikin abubuwan da aka shirya za su sami Sarkin Kano Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi II domin idan ka yi nazarin yadda Ganduje ya dage yana wannan aikin kai ka ce wahayi ne ayi masa saboda babu batun saukakawa yi kawai yake yi sai inda birki ya katse.

Ya zuwa yanzu Gwamna Ganduje baya sauraran kowa, baya jin maganar kowa yana son ya tabbatar aikin da aka bashi ya kaddamar kuma an yi nasara, an bashi sakamako, ko ba komi batun murdiyar zabansa da ake zargi yana gaban kuliya manta sabo kuma wadanda suka sa shi wannan aika-aika sune ke da ta cewa akan batun shari’ar kasar nan, tunda kwana kwanan nan muka ji ana zargin tauraruwa mai wutsiya da bada cin hanci a sokin zaban jihar Osun, jihar Kano ma Allah Ya sawaka.

Magana ta  biyu wanda nake da ra’ayin ta haifar da wannan darbarwa idan na karkare wannan a sati mai zuwa sai fara kawota wato batun daukar hankalin ‘yan arewa akan bala’I’in da suke fama da shi na satar jama’a domin neman kudin fansa da fashi da Makami da satar shanu da kai hare-haren kunar bakin wake ba gaira babu dalili amma yanzu batun masarautar jihar Kano ya fara dauke hankalin ‘yan arewa da duniya baki daya. Mu hadu a mako mai zuwa Insha Allahu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!