Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wani Dalibi Ya Mutu A Ruwan Wankan Otal

Published

on

Wani dalibin jami’ar kwalejen kimiyya ta Jihar Kuros Ribas, wanda ya ke karatu a fannin bayar da sawarwari mai suna Ogbe Dominic, wanda ake yi wa lakabi da Pogba, ya nutse a ruwan wankan otal a Kalaba. Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a lokacin da dalibin tare da sauran dalibai suka je gasar yin wanka.

Wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa wanda ya bayyana cewa shi abokin mamacin ne, ya bayyana cewa mamacin tare da sauran daliban jami’ar kwalejin kimiyya na Jihar Kuros Ribas da ke garin Kalaba, sun gudanar da fati a ranar Juma’a da yamma a otal din ‘Jacaranda Suites’ da ke yankin Atimbo cikin garin Kalaba, inda ya nutsa a cikin ruwan wankan otal, sannan ya mutu har lahira. Ya kara da cewa, mamacin ya doke abokin karawarsa na jami’ar Kalaba a gasar wanka, amma sai ba a ganshi ba bayan kammala gasar. “ Mun kammala gasar wankan ke nan, inda kowa ya fito daga cikin ruwan, amma ba mu ga fitowar Pogba ba. Mun jira na tsawan lokuta har sai da lakacin da mahukuntar otal din suka tsamo shi a cikin ruwan. Duk da yunkurin ceton ransa da aka yi, yana ta aman jini, gari da kuma gyada daga bakinsa tare da hawaye ya mamaye masa fuska. Likita ya tabbar da mutuwar Dominic ne, lokacin da aka kai shi asibitin koyarwa na jami’ar Kalaba,” in ji wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa.

Shi dai mamacin Ogbe Dominic, dan asalin karamar hukumar Obudu na Jihar ne, sannan kuma dalibi ne da ya ke karatu a sashi bayar da shawarwari na jami’ar kwalejin kimiyya da ke Kalaba.

Lokacin da majiyarmu ta ziyarci otal din a ranar Lahadi, ana gudanar da harkoki ba kamar yadda aka saba ba, yayin da mutane suka yi cin-cirindo suna tattauna lamarin duk da hukumomin otal din sun ki yin bayani a kan lamarin. “Wannan shi ne karo na biyu da dalibai suke nutsewa a ruwan wankan otal din ‘Jacaranda Suites’ .

Da farko dai, wani dalibi na jami’ar Kalaba wanda shi kadai ne yaro daga wajen iyayansa ya mutu a wannan ruwan wankan otal din,” in ji majiyarmu.

Majiyarmu ta tuntubi kakakin jamiar kwalejin kimiyyar na Jihar Kuros Ribas, Onen E. Onen a ranar Litinin, inda ya tabbatar da wannan labara. “Na samu labarin lamarin, amma ina bukatar ku bani lokaci domin in samu izini daga wajen shugaban jami’ar, Farfesa Akon Joshua, kafin in yi magana a kan lamarin da ku.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!