Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

‘`Yan Siyasar Amurka Na Fakewa Da Maganar Sata Suna Yaudarar Kansu’

Published

on

Kwanakin baya wasu ‘yan siyasa na Amurka sun bayyana cewa, kasarsu wurin adana kudi ne, daukacin kasashen duniya, ciki har da kasar Sin suna satar kudi ne daga kasar, sun fadi haka ne domin ba su da ilimin tattalin arziki, kuma suna yaudarar kansu ne.

Tsarin kasuwa ya nuna cewa, idan sassa biyu suka yi sayayya a tsakaninsu, to za su samu riba daga sayayyar tare, haka ma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka. A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana shigo da injunan lantarki da kayayyakin amfanin noma da yawan gaske daga Amurka, saboda ita kanta tana karancin irin wadannan kayayyaki, ita kuma Amurka ta samu damar zuba jari da kuma habaka kasuwa a kasar Sin, a sanadin haka, Amurka ta ingiza ci gaban tattalin arzikinta kamar yadda take so.

Amma Amurka ba ta fahimci hakan ba, sai ta rika sukar kasar Sin wai tana satar fasahohi da guraben aikin yi da kuma jari daga Amurka, kuma wai ta yi hakan ne domin tana neman wani dalili ne yayin da take kara buga haraji kan kayayyakin kasar Sin.

To kada Amurka ta manta, ba zai yiyu ba ta cimma burinta ta har sharara karya, ta yadda kullum za a ce ita ce mai gaskiya.

Alkaluma sun nuna cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Amurka ta samu riba mai tsoka daga kasuwar kasar Sin, misali a shekarar 2017, adadin kudin da kasar Sin ta baiwa Amurka domin kare ‘yancin mallakar fasaha ya kai dala biliyan 7 da miliyan 130, adadin da ya kai kaso 25 bisa dari cikin daukacin kudin da kasar Sin ta biya sauran kasashen duniya a wannan fannin. A halin da ake ciki yanzu, adadin kudin da kamfanonin Amurka suka samu daga sayar da kayayyakinsu ya kai dala biliyan 700 a kowace shekara, adadin ribarsu ya kai dala biliyan 50. Daga shekarar 2008 zuwa 2017, karuwan kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa kasar Sin ta kai kaso 86 bisa dari, amma a makamantan lokacin, karuwar kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa sauran kasashe kaso 21 kawai bisa dari.

Yanzu ana amfani da dala yayin da ake gudanar da harkokin cinikayya a kasashen duniya da suka kai kaso 70 bisa dari, a sakamakon haka, Amurka tana amfani da wannan fiffikon domin kara samun riba daga karuwar tattalin arzikin sauran kasashe, wato al’ummun kasar ta Amurka wadanda da suka kai kaso 4.4 bisa dari daga cikin daukacin al’ummun kasashen duniya suna amfani da hajojin da suka kai kaso 22 bisa dari dake na daukacin hajojin duniya, wannan na nuna cewa, suna kwace sakamakon karuwar tattalin arzikin duniya, me ya sa ‘yan siyasar Amurka ba su taba bayyana wannan lamarin ba?

A don haka ana iya cewa, satar da suke fada karya ce kawai, an kuma lura cewa, sun fadan haka ne domin su damu da tangardar din da Amurka ke ciki a bangaren hada-hadar kudi.

Shahararren masani tattalin arzikin Amurka Stephen S. Roach ya yi nuni da cewa, Amurka tana fakewa da kasar Sin ne kamar yadda ta ke bukata, saboda zai yi wahala ta daidaita matsalar da take fuskanta, yanzu haka idan ana son daidaita huldar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, ya dace sassan biyu su yi kokari tare domin samun moriya tare.

An lura cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje shekaru 40 da suka gabata, kuma ta samu sakamakon ne bisa dogaro da kanta, amma ba sata ko neman taimako ba, ko shakka babu karyar satar da ‘yan siyasar Amurka suka fada ba za su yaudari al’ummun kasashen duniya ba, balle ma su hana ci gaban kasar Sin, ko shakka babu kasar Sin wadda ke kara bude kofa ga kasashen waje za ta ci gaba da himmantuwa domin kara kago abubuwan al’ajabi a nan gaba.

(Jamila)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!