Connect with us

WASANNI

’Yan Wasan Afrika Sun Yi Bajinta A Gasar Firimiyar Ingila

Published

on

Sadio Mane na Liverpool da Pierre-Emerick Aubameyang na Arsenal sun ci kwallaye a wasan karshe na gasar firimiya domin su raba kyautar takalmin gwal ta dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a tsakaninsu.

Aubameyang ya ci wa Arsenal kwallo biyu a wasansu da Burnley, wanda hakan ke nufin ya kamo Salah da abokin wasansa Mane a matsayin wadanda suka fi kowa zura kwallaye a gasar firimiyar bana da aka kammala ranar Lahadi.

Kowannensu yana da kwallaye 22. Mane ya ci kwallo ta 21 da 22 a wasan karshe da Liverpool ta ci Wolves 2-0 kuma wannan ne karo na farko da sama da mutum biyu suka lashe kyautar tun bayan Dimitar Berbatov da Carlos Tevez da suka lashe Golden Boot din a shekarar 2010 zuwa 2011 da kwallo 20 kowannensu.

Dan wasan Gabon Aubameyang, wanda ya ci kwallo biyu shi ma a filin wasa na Turf Moor ya ce sun raba wannan kambu da ‘yan wasa biyu da suke burge shi kuma zakakuran ‘yan wasan Afirka. Saboda haka su wakilan Afirka ne.

Yaci gaba da cewa ya ji dadi sunyi nasara abokan wasansa suna sane da kyautar amma baice masu komai ba saboda baya so su dogara da shi kadai gara su yi aiki tare domin kungiyar tasamu nasarar da ake bukata

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya nuna jin dadinsa ga tsohon dan wasaan Dortmund Aubameyang, wanda ya siyo shi a shekara ta 2013 daga Saint-Etienne lokacin yana kociyan Borussia Dortmund.

Salah mai shekara 26 ya ci kwallo 32 a kakar bara kuma ya kafa tarihi, domin shi ne dan wasan da ya fara cin kwallo 32 a wasanni 38 shi ne kuma dan wasa na shida da ya lashe kyautar a kaka biyu a jere.

Dan wasa Harry Kane na Tottenham da ya lashe kyautar sau biyu a jere a shekarun 2015 zuwa 2016 da 2016 zuwa 2017, ya kare kakar bana da kwallaye 17, kakar da ya sha fama da rauni kuma har yanzu yana jinya duk da cewa zai iya buga wasan karshe na kofin zakarun turai da kungiyarsa zata fafata da Liverpool a wata mai kamawa..
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!