Connect with us

LABARAI

Zamfara: Kullum Sai Mun Biya Fansa Ga Barayin Shanu – Karamar Hukumar Shinkafi

Published

on

Mataimakin shugaban karamar hukumar mulki ta Shinkafi da ke jihar Zamfara, Alhaji Sani Galadima, ya bayyana cewa, a kullum sai sun biya barayin shanu kudin fansa, saboda tserar da rayuwar al’umma, inda ya karawa da cewa, bada jimawa ba ’yan ta’addar sun kashe jami’an tsaro shida.

Galadiman ya bayyana wannan ne ranar Litinin ga ministan harkokin cikin gida, Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, sa’ilin da ministan ya ziyarci jihar ta Zamfara kan batun matsalar tsaro da ke addabar yankin tare da sauraron koke da korafe-korafe al’umma kan lamarin.

Daga cikin guraren da ministan ya ziyarta a lokacin ziyarar, akwai garin karamar hukumar mulki ta Bungudu, inda ya sauka a fadar sarkin garin, Alhaji Hassan Attahiru, inda a nan, al’ummar masarautar da masu hannu da shuni su ka bayyana wa ministan irin matsalolin da su ke fuskanta.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, wato NAN, ne ya ruwaito kalaman Galadiman na Shinkafi ga Minista Dambazau kan matsalolin da su ke fuskanta a sa’ilin ziyarar, inda a ciki ya bayyana cewa, a sakamakon aikin barayin shanu da masu garkuwa da mutane, kullum ne sai sun biya kudin fansa, in ji shi.

“Jami’an tsaro shida ’yan bindigar su ka kashe a ranar Lahadi lokacin da maharan ke kan hanyar komawa a muboyarsu cikin daji bayan sun shigo gari karbar kudin fansa. Ko a ranar Lahadin, ‘yan bindigar sun aiko wa hakimin garin Shinkafi da wasika, cewa za su zo su kawo hari a garin.

“Wannan mummunan yanayin da mu ka samu kanmu a ciki ya na da ban tsoro matuka, kullum safiyar Allah sai mun biya miliyoyan kudi a matsayin kudin fansa ga wadannan maharan. Hakika mu na bukatar tsananin agajin gwamnati, domin kawo karshen wannan matsalar,” in ji Galadima ga Dambazau din.

Ya cigaba da cewa, “matanmu na shan wahala sosai, domin idan maharan sun kawo hari, bayan sun gama su kan dauke matan su tafi da su a gaban iyayensu ko mazajensu. Yanzu, sam mutane a karamar hukumar mulki ta Shinkafi ba ma iya bacci cikin natsuwa.”

Ya yi kira da cewa, “mu na son gwamnati ta kawo gyara kan matsalar karancin jami’an tsaro a kauyen namu. A garin nan gabadaya, soja 19 kadai ke cikinsa. Mu na bukatar agajin gaggawa daga gwamnati. Lallai mu ba mu gamsu da iya abinda jami’an tsaro ke yi ba.

“Kowa ya san inda barayin shanun nan su ke zama; hatta jami’an tsaron ma sun san muboyarsu. Abinda ke ba mu mamaki shi ne, jami’an tsaron ba sa zuwa su riski maharan a inda su ke.”

Galadiman ya kuma yi fata da cewa, “mu na fata sakamakon wannan ziyarar, matsalar da mu ke fuskanta za ta kawo karshe.”

A bayanin na mataimakin shugaban karamar hukumar, ya bayyana cewa, hare-haren barayin shanun ya yi sanadiyyar tarwatsa kauyuka akalla 98 a cikin yankin karamar hukumar ta Shinkafi.

A nasa jawabin, Minista Dambazau, cewa ya yi, “wannan ba shi ne zuwana na farko a jihar ba. Mun fara wannan ne domin ganin mun kawo karshen matsalar tsaron, ba ma a jihar ta Zamfara kadai ba, a’a, har da sauran wurare.

“Shugaban kasa ne ya umurce ni da na ziyarci masarautun Shinkafi da Anka, domin ji da ganin abubuwan da ke faruwa, don daukar mataki. Haka kuma, shugaban kasar ya ce, na isar da sakon ta’aziyarsa ga al’ummar yankunan bisa rasa dukiyoyi da rayuka sakamakon abubuwan da ke faruwa.”

Dambazau ya ce, “hakkin gwamnati ne ta samar da tsaro tare da kiyaye dukiyoyi da rayukan al’umma. Kan haka ya zama wajibi mu ga mun yi abin da za mu iya, don samar da hakan.”

Ya ci gaba da cewa, “Mun fara wannan yunkurin ne da fara zama da kungiyar Miyetti Allah, daga baya za mu gana da sarakunan gargajiya tare da gwamnonin jihohin da abin ya fi shafa.”

A ziyararsa zuwa fadar Sarkin Bungudu, Alhaji Attahiru, bayan yaba wa ministan bisa ziyarar da ya kawo. Sai sarkin ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wurin magance matsalar.

A garin Anka ma haka, masu hannu da shuni da manyan gari, a yayin ganawa da ministan a fadar sarkin garin, Alhaji Attahiru Ahmad, sun koka ma sa da irin matsalar tsaron da su ke fama da ita a garin.

Sarkin, a jawabinsa, ya bayyana cewa, akalla mutane mazauna kauyuka 13,000 ne su ka gudu daga kauyukansu sakamakon hare-haren ’yan bindigar, ya kuma ce, ya zama dole gwamnati ta yi gaggawar daukar mataki domin jama’arsa su samu iya zuwa yin noma a gonakinsu.

“Mun ji dadi da ministan harkokin cikin gida ya kawo ma na ziyara, domin ganin halin da mu ke ciki tare da jajenta ma na kan bala’i da musifar da mu ke fuskanta. Da wannan ziyarar taka, fatanmu na samun sauki daga abinda mu ke fuskanta ya samu,” in ji Sarkin.

Ya cigaba da cewa, “an kashe ma na mutane da yawa, ba kadan ba, tare da yin garkuwa da wasu. A halin yanzu da na ke maganar nan, mu na da akalla mutane 13,000 mazauna kauyuka da su ka gudu su ka bar gidajensu zuwa nan garin Anka. Ba nan kadai ba, akwai wasu masu yawa a wasu kauyukan da garuruwa. Wasu kuma sun gudu gabadaya sun bar jihar.

“Yanzu noma ba ya yiyuwa, saboda mutane sun gudu sun bar kauyukansu. Sai idan har gwamnati ta iya yin wani abu kan lokaci, to sannan ne kawai zai yiwu. Da yawan mutane, to ba za su samu damar yin noma ba.”

Ministan, a nasa jawabin, ya yi jan kunne ga maharan da imma su yi saranda ga jami’an tsaro ko kuma a kashe su. Ministan ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da matakai da hanyoyin da za ta bi, don magance matsalar tsaro a jihar da ma sauran wasu jihohin.

Ministan ya fada wa sarkin cewa, “Shugaban kasa Buhari ya damu matuka da abinda ke faruwa a Zamfara, dalilin da ya sanya ya turo ni kenan.

“Ina mai tabbatarwa da al’ummar Zamfara cewa, bada jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta kawo karshen barayin shanu da masu garkuwa da mutane.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!