Connect with us

LABARAI

An Tsare dan Shekaru 27 A Bisa Tuhumar Sa Da Kisan Kai

Published

on

Wata kotun Majistare ta Ebute Meta a Legas ta yi umurni da a tsare wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa mai suna Monday Odeh a gidan yari bisa tuhumar sa da aikata kisan kai. Alkalin kotun, Mista O.O. Olatunji, ne ya yi umarni da a tsare shi a gidan yarin na Ikoyi har zuwa lokacin da kotun za ta sami shawara daga ofishin daraktan shari’a na jihar.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun, Sufeto Oladele Adebayo, ya shiada wa kotun cewa, wanda a ke tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Afrilu, a Anguwar Magodo, da ke Legas. Ya kuma yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya yi amfani ne da cebur ya buge mamacin mai suna, Abdullahi Yunusa mai shekaru 54, da shi a kai wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
A cewar shi, laifin ya sabawa sashe na 222 na dokar aikata laifuka ta Jihar Legas, 2015. Mai shari’a Olatunji, ya dage sauraron shari’ar har zuwa ranar 17 ga watan Yuni.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!