Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Andrea Bocelli Ya Rera Wakar Nessun Dorma A Yayin Bikin Nunin Al’adun Asiya

Published

on

A daren Laraba, shahararren mawakin Italiyan nan Andrea Bocelli ya rera wakar wasan kwaikwayon Turandot mai suna Nessun Dorma yayin bikin nunin al’adun Asiya.

A Talata da yamma ne Andrea Bocelli ya bayyana a wurin atisayen bikin dake gudana a filin wasannin na Bird’s Nest yayin da yake zantawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG a takaice cewa, wakar Nessun Dorma tana da muhimmanci a bangaren wasan kwaikwayon duniya. Ya sha rera wakar a kasar Sin, yanzu haka zai sake rera wakar a filin nunin al’adun Asiya mai muhimmanci matuka.

Andrea Bocelli ya kara da cewa, kide-kiden kasar Sin suna taka babbar rawa a dandalin kide-kiden duniya, sanin kowa ne cewa, Sinawa suna kishin kide-kiden kwarai.

Ya ce, yayin ziyararsa a kasar Sin, ya kara fahimtar muhimmancin cudanyar wayewar kai tsakanin kasa da kasa, saboda kide-kide harshe ne da al’ummun kasashen duniya suke yin cudanya maras shinge, a don haka kide-kide za su taimaka wajen fahimtar juna tsakanin al’adu dabam dabam, kuma wani bangare ne na tushen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.

(Jamila)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!