Connect with us

LABARAI

Ba Da Mu Za A Yi Wa Buhari Juyin Mulki Ba, Cewar Hedikwatar Tsaro

Published

on

A ranar Talata ce Shalkwatar tsaro ta kasa ta tsame kanta daga wata takarda da ke yawo, wacce ta ke yin kira da a hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hula ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Mataimakin daraktan sadarwa na shalkwatar tsaro ta kasa, Nebi Kyaftin Muhammed Wabi, ya zargi wata kungiya mai suna, ‘Nigerian Continuity and Progress’ (NCP) da cewa su ke yada takardar.
Wabi ya yi zargin cewa, takardar wai ta na yin kira ne da a kafa gwamnatin rikon kwarya a maimakon zababbiyar gwamnati.
“Rundunar Sojojin Nijeriya tana mai farin cikin tsame kanta daga wata takardar banza wacce ke kunshe da maganar banza a cikinta da wata kungiya, wacce ba a san ta mai suna Nigerian Continuity and Progress (NCP) ke yadawa, inda su ke yin kira da a yi juyin mulkin da zai ture zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya ta farar hula mai ci a halin yanzu, a makwafinta, a kafa gwamnatin wucingadi.
“Kai tsaye, Rundunar Sojin Nijeriya ta na yin Allah-wadai da masu kira ga wannan aikin da ya saba wa tsarin dimokuradiyya da masu rubuta wannan takardar su ka yi.
“Haka nan kuma, a na bukatar al’umma su yi watsi da wannan takardar da kuma dukkanin abinda ke cikinta, kamar yadda wannan kungiyar ke yin yawo da ita, kuma su yi tir da Allah-wadai da duk wani kira na rushe abinda mu ka yi aiki tukuru na tabbatar da shi a bisa tafarkin dimukradiyya.
Wabi ya ce, shalkwatar tsaron ta na sane da aikin da ya hau kanta kamar yadda tsarin mulki ya dora mata, “ba kuma za ta zame zuwa wani abinda zai lalata tafarkin dimukradiyya ba, kamar yadda ya ke a cikin tsarin mulkin 1999, wanda a ka yi wa kwaskwarima.
“Shalkwatar tsaro ta kasa ta na mai cikakken biyayya ga abinda tsarin mulki ya tanada, ta na kuma mai cikakkiyar biyayya ga Shugaba Buhari, kuma babban Kwamandan dakarun tsaro na Nijeriya,” in ji shi.
Sanarwar ta ce, dukkanin hukumomin tsaro da su ka dace an shawarce su da su zakulo wadanda su ke da hannu a kan rubutawa da kuma raba wannan mummunar takardar domin daukan matakin da ya dace a kansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!