Connect with us

LABARAI

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta NHRC Ta Yi Tir Da Kama Karuwai A Abiya

Published

on

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa wato NHRC ta yi tir da kama karuwai a garin Umuahia babban birnin jihar Abiya tare da kulle wuraren badalar da ‘yan sanda suka yi bisa umurnin gwamnatin jihar Abiya,.

Uche Nwokocha, Kodinetan hukumar NHRC din reshen jihar Abiya shi ne ya yi wannan Allah-wadai din, inda ya bayyana hakan a matsayin kokarin gwamnati da jami’anta na maishe da talauci laifi.

Nwokocha ya tabbatar da hakan ne a jiya Laraba a yayin zantawarsa da manema labarai. Rahotanni sun tabbatar da cewa; gwamnatin jihar ne suka ba da umurnin rufe dukkanin gidajen karuwai da ke daukacin birnin jihar. Inda suka bayyana wuraren a matsayin wata mafaka na bata gari. Sannan har wala yau, gwamnatin jihar ta baiwa jami’an tsaro damar rushe dukkanin gidajen karuwan da kuma inda ake zargin cewa mafakar bata garin ne, lamarin da ya janyo ‘yan sanda suka kame karuwan ke nan.

Har wala yau sai dai shi shugaban NHRC din reshen jihar, ya bayyana hakan a matsayin wani mataki na take hakkin bil’adama, ya ce; kama wadannan ‘yan matan ya faru ne sakamakon Talakawa ne. Ya ce; akwai wadansu matan da suke irin sana’arsu a wadansu wuraren, amma ba a kama su ba. Ya ce; “wadannan Talakawa ne kawai aka kama su.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!