Connect with us

LABARAI

Manoman Doya Sun Nemi Gwamnati Ta Kulla Yarjejeniya Da Tarayya Turai

Published

on

Kungiyar masu noman doya da sarrafata da kasuwancinta ta kasa, sun nemi gwamnatin tarayya da ta kulla wata yarjejeniyar kasuwancin tsakaninta da tarayyar Turai domin samar da hanyar mafi sauki wajen fitar da doyan zuwa kasashen Turai.

Kungiyar tare da hadin guiwar Kwamitin da ke kula da fitar da Doya sune suka fitar da hakan jim kadan da kammala wani yawon gani da ido na kwanaki hudu da sashen masu ruwa da tsaki suka kai wurin masu safarar Doya na kasar Ghana.

Rahoton wanda Farfesa Simon Irtwange, shugaban kungiyar, kuma jagoran Kwamitin fitar da Doyan ya sanyawa hannu, ta nuna yadda kasar Ghana ta sanya hannu daban-daban da Tarayyar Turai, wanda yake bai wa masu safarar Doya zuwa kasashen Turai damar kai wa cikin sauki cikin harda Birtaniya daga kasar Ghana. Bayanin ya ce; wannan ziyarar da suka kai zai ba su damar Nijeriya ta samu ilimin fahimtar matakin da kasar Ghana ta dauka wanda ya sa suka samu nasarar sarrafa Doyan su, adana su, da kuma safarar su zuwa kasashen Turai. Ya ce; wannan ziyarar ta su zai sanya Nijeriya ta samu karin haske. Ya ce; Nijeriya na da bukatar ta bunkasa yadda take fitar da Doya zuwa kasashen waje  ta yadda Doya zai zama daya daga cikin manyan kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa wanda zai bunkasa kudaden da gwamnati ke samu daga kasashen waje.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!