Connect with us

RIGAR 'YANCI

Masu Nadin Sarkin Kano Sun Gayyato Lauyoyi Masu Daraja Ta Daya Don Kalubalantar Ganduje

Published

on

Masu Nadin Sarkin Kano sun gayyato Lauyoyin 7 Masu Mukamin SAN da kuma wasu Lauyoyin guda 17 domin kalubalantar matakin Gwamna Ganduje na kirkirar sabbin Masarautu hudu daga Masarautar Kano, masu karar sun hada da Madakin KanoYusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Ibrahim, Sarkin Dawaki mai tutu Bello Abubakar da Sarkin Bai Muktar adnan wanda suka shigar da kara ranar Talata a gaban wata babbar kotu a Kano, wanda suke kalubalantar kakakin Majalisar dokokin JIhar Kano.

Gwamnnan Kano, Kwamishinan Shari’a tare da sarakuna hudu da Gwamnan ya nada. Sunayen Lauyoyin da Masarautar ta Kano ta gayyato sun hada da  Prince Lateef Fegbemi, SAN, FCIArb,(UK), AB Mahmoud, OON, SAN, FCIArb, (UK), Adeniyi Akintola, SAN, Suraj Sa’eda, SAN, Hakeem O. Afolabi, SAN, Paul Usoro SAN, Nassir Abdu Dangiri, SAN, Others are Maliki Kuliya Umar Esk, Nureini S. Jimoh Esk, Dr. Nasiru Aliyu Esk, Sagir Gezawa Esk, Muritala O. Abdulrashek Esk, Aminu S. Gadanya Esk, Ismail Abdulaziz Esk, Rashidi Isamotu Esk, Oseni Sefullahi Esk, Ibrahim Abdullahi Esk, Haruna Saleh Zakariyya Esk, Auwal A. Dabo Esk, Badamasi Sulaiman Esk, O. O. Samuel Esk, Fariha Sani Abdullahi, Yahaya Isah Abdulrasheed, ACIArb, (UK) da Amira Hamisu.

A cewar masu karar kokarin samar da dokar kirkirar sabbin masarautun hudu barazana ne ga tarihin masarautar Kano, musamman idan a ka yi la’akari da mukaman da suke rike dashi a masarautar. Haka kuma sun ce mukaman da suke rike dasu na da danganta ka da gidan Jobawa, Sullubawa. Yolawa da Kuma Dambazawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!