Connect with us

LABARAI

NAFDAC Ta Yi Gargadi Kan Jabun Maganin Mura Da Ke Yawo A Gombe

Published

on

Hukumar da ke kula da abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC a yau Alhamis ta bayyana cewa jama’a su yi hattara da wani maganin mura da yake yawo a jihar Gombe. Hukumar ta ce; akwai wani jabun magani na Mixagrip da ke yawo a jihar.

Wannan sanarwar ta fito ne a wata sanarwar da Farfesa Moji Adeyeye, Babbar Daraktar hukumar ta NAFDAC din ta fitar a birnin tarayya Abuja. Adeyeye ta ce an gano wannna jabun maganin ne a yayin wani atisaye da hukumar ta gudanar a cikin garin Gombe. Ta ce; an gano maganin ba shi da suna da kuma adireshin inda aka sarrafa maganin. Ta ce; a maimakon a rubuta sunan Kamfanin da aka yi maganin da adireshinsa, sai kawai aka rubuta cewa an sarrafa shi ne a ‘India for Afrowell Exports Mumbai, India.’

“Wadansu bayanan da maganin ke dauke da shi an yi rubutu kamar haka; Code No. -MH/DRUGS/MH/101063A; Batch No. – V18635; Manufacturing date – 10/2018 with Expiry date reading 09/2021,” Inji Adeyeye.

Sai dai ta ce asalin maganin an sarrafa shi ne a Nijeriya wanda kamfanin Orange Kalbe Limited mai adireshi kamar haka 66/68 Town Planning Way, Ilupeju, Jihar Legas.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!