Connect with us

KASUWANCI

NERC Taci Kamfanin AEDC Tarar Naira Miliyan 300

Published

on

Sakamakon gazawar sa na kasa samo kadarar rabar da wutar lantarki daga fanni na uku, inda har hakan ya janyo mutuwar wani yaro dan shekara hudu a jihar Nije, Hukumar samar da wutar lantarkinta kasa NERC taci kamfanin rabar da wutar lantarki dake Abuja AEDC tarar naira miliyan 300.

Hukumar ta NERC ta sanar da hakan ne a cikin sanarwar data fitar ta a garin Abuja, inda ta kara da cewa, daga cikin tararar ta naira miliyan 300, za’a kuma biya iyayen yaron marigayi Mohammed Arafat Jibril, diyyar naira miliyan 50 saboda rasa dansu da sukayi da tarasfor wutar da kamfanin ya bari a bude ta babbake shi.

Takardar ta cin tarar da jaridar Thisday ta samo daga gun Hukumar a garin Abuja ta sanar da cewar, sauran laifin da kamfaninnna na AEDC ya tabka ya hadada, sakacin kamfanin da ya janyo mutuwar yaro a ranar 11 ga watan Afirilun shekarar 2019,na rashin kulle Murfin akwatin rabar da wutar ta dake a rukunonin gidaje na manyan ma’aikata na tarayya dake a yankin Maikunkele, cikin karamar hukumar Bosso a jihar Neja.

Acewar Hukumar ta NERC, Mohammed ya gamu da ajalinsa ne saboda jan da wutar lantarkin tayi masa mai karfin 300 (kBA) 11/0.415kBA a yankin na Maikunkelel dake turo karfin wutar lantarki 33/11 kB l.

Acewar Hukumar ta NERC, sashe na 1.3.26 sakin layi na shida na hukumar na tsarin rabar da wutar lantarki, ya dorawa kamfanonin na rabar da wutar lantarki dake garin Abuja nauyim cewar, dole ne tun daga kan tarasfomomin su, makashin wutar su, da kuma akwatinan su na raba da suka kakkafa akan hanyoyi da kuma inda mutanen gari zasu iya ganin su a fili, dole ne su basu kariyar data dace don gujewa aukuwar hadurran wutar ta lantarki, musammkkulle kofofin akwatunan wutar ko kuma su sanya masu shinge ko kima dukkan daukar matakan da suka dace na bayar da kariya.

Acewar Hukumar ta NERC, wuce sanya kayan kariya, akwai kuma bukatar sanya alamu da kamfanonin rabar da wutar lantarkin ya kamata suyi na killace na’urorin rabar da wutar, da zasu nuna yin gargadi ga mutane na aki yaye hadduranndake tattare da shiga cikin na’urorin rabar da wutar lantarkin.

Hukumar ta sanar da cewar, sashe na 5.3.1 na kiwon lafiya da bayar da kula na bangaren NEHSC ya bukaci kamfanin na AEDC ya tura rahoton sa a cikin awa 72 bayan da lamarin ya rutsa da Mohammed har ta kai ga mutuwar sa, amma kamfanin ya gaza yin komai akai.

Hukumar ta kuma soki kamfanin n AEDC akan yin sakacin bin ka’idojin samun lasisin sa na rabar da wutar lantarki da tsarin lafiya na HSC, inda hakan ya janyo mutuwar yaro dan shekara hudu Mohammed Arafat Jibril, a ranar 11 ga watan Afirilun shekarar 2019 a rukunonin gidaje na manyan ma’aikata na tarayya dake yankin Maikunkele, a cikin karamar hukumar Bosso cikin jihar Neja.

Hukumar ta NERC tace, kamfanin na AEDC tabka sakaci wajen sauke nauyinsa na daukar matakan da suka dace na baiwa alumar gari kariyar jefa rayuwar su a cikin matsala ta hanyar baiwa tsarin su na rabar da wutar kariyar data kamata kamar yadda dokokin Hukumar ta tanadar, inda hakan ya janyo wutar taja Mohammed Arafat Jibril har ya rasa ransa.

Hukumar tace, kamfanin na AEDC ya gaza tura rahoton sa na farko akan aukuwar lamarin a cikin awanni 72, inda hakan ya sabawa sashi na 5.3.1 na kiwon lafiyar tsarin HSC, kuma hakan, sabawa dokokin Hukumar ta NERC ne da sauran ka’idojin ta, inda hakannya janyo mutuwar yaron kuma dole ne kamfanin ya ya biya iyayen yaron Mohammed Arafat Jibril diyyar naira miliyan 50 kuma kamfanin , zai mika kudin ne ga iyayen yaron a shalkwatar Hukumar a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2019.

Acewar Hukumar, dole ne kuna kamfanin nan AEDC ya biya tarar naira miliyan 250 ga Hukumar saboda karya dokokin ta, ida Hukumar tace, dole ne kuma kamfaninnya biya wannan tarar a ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2019.

Har ila yau, Hukumar ta NERC ta umarci kamfanin ya gabatar mata da cikakkun bayanai akan ayyukan sa na samar da kariya ya kuma tura mata a cikin kwanuka 90.

Bugu da kari, Hukumar ta NERC ta nuna bayanan samar da kariya a garin na Abuja na kamfanin Disco daga shekarar 2018 zuwa shekarar 2019, inda tace, an samu mutuwar mutane tara da wadanda suka kone su biyu.

A wata sabuwa kuwa, Hukumar ta NERC ta kuma ci kamfanonin rabar da wutar lantarki Disco dake jihar Legas tarar naira ko wannen su 10,000 a bisa zargin rabar dawutar lantarki ga masu amfai da ita ta haramtacciyar hanya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!