Connect with us

KASUWANCI

NNPC Ta Kwato Dala Biliyan 1.6 Daga Hannun Kamfanoni – Baru

Published

on

A ranar Talatar data gabata, Manajin Darakta na rukunonin kamfanin NNPC Dakta Maikanti Baru, ya yi shelar cewar, kamfanin ya kwato dala biliyan 1.6 daga gun wasu kamfanoni da wasu sassan kamfanin yake bi bashi.

Dakta Maikanti Baru ya sanar da hakan ne a babban birnin tarayyar Abuja a lokacinnda yake amsa tambayoyin manema labarai a lokacin jami’an Cibiyar kwararru ta kasa CIFIPN ta kai masa ziyar ban girma da kuma bashi lambar karramawa data uban Cibiyar, tare da bukatar da Cibiyar ta nema na yin hadaka da kamfanin na NNPC.

Cibiyar ta CIFIPN tana yin yaki ne da yin damfara kuma tana bayar da horo ga kwararru a bangarori da dama a fannin kimiyya da fasaha da kuma bankado aikata dukkan wata badakala da kuma samar da matakai don kare kara aikata hakan a nan gaba.

Acewar Dakta Maikantin Baru, kamfanin a karashin sashen sa na NPDC da kuma yake a karkashin kulawar kamfanin na NNPC, an samu cin babbar nasara wajen bankado tabka almundaha da kuma kare kara aukuwar hakan, inda ya yi nuni da cewar, sakamakin hakan, an samu cin nasara wajen tsaftace masana’antar.

Dakta Maikanti Baru yaci gaba da cewa, “Saboda ayyukannda muke gudanarwa, mun iya samun kamfanonin Atlantic da sashin NNPC ke binsu basussuka, NPDC, inda suka maido bashin dala biliyan 1.6 ga NPDC, mun kuma yi namjin kokari wajen dakile aikata badakala.”

Manajin Daraktan yace, akai dinbin shari’oi a gaban kotu da kamfanin ya shigar na aikata badakala da ban-da-ban, kuma zakayi mamaki in kaga irin kudin dake a ciki, domin idan baka da mutane dasuke da kishi na yaki da cin hanci da rashawa, da an cinye mana sama da dala biliyan 1.6.”

Acewar sa, “ Muna da shari’u da dama kamar ta tsakanin kamfanin NNPC da IPCO, inda suke bukatar sama da dala miliyan 400 saboda ayyukansu, amma mun samu shawo kan hakan a bayan kotu dasu akan dala miliyan 37.5.

Dakta Maikanti Baru ya kara da cewa, an samu cin nasarar kwato basussukan ne a bisa jajircewar ma’aikatan kamfanin na NNPC da kuma sauran abokan kasuwancin sa da suka rungumi dabi’arbin ka’ida da yin gaskiya a yayin gudanar da ayyukansu.

Da yake yin tsokaci akan lambobin karrawar da Cibiyar ta CIFIPN ta bashi, Dakta Maikanti Baru ya baiwa Cibiyar tabbacin cewar zai basu goyon bayan da ya dace na kwarewar sa yadda zasu kara inganta binciken a daukacin fadin kasar nan.

A nata jawabin tunda farko, Shugabar rikon kwarya ta Cibiyar ta CIFIPN Dakta Bictoria Enape tace, Cibiyar ta jima tana bibiyar ayyukan da Manajin Daraktan kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru tun lokacin da aka nada shi akan mukamin.

Acewar Dakta Bictoria Enape “Munzo ofishin ka ne don mu gode maka akan kokarin da kake yi na yaki da cin hanci da rashawa a kamfanin na NNPC, musamman, ganin kaine tsohon Shugaban kwamtin yaki da cin hanci da rasha a yanzu kuma Manajin Darakta na rukunonin kamfanin NNPC.”

Dakta Bictoria Enape ta kara da cewa, “Munyi imani, kamfanin NNPC dama ya kamata ace baida wata alaka da cin hanci da rashawa ginin cewar, mutum kamar ka ya jima yana yin yaki da cin hanci da rashawa.”

Shugaba Dakta Bictoria Enape ta sanar da cewar, Cibiyar ta CIFIPN tana son yin hadaka da kamfanin na NNPC da Hukumar hana fasakauri ta kasa da sashen albarkatun mai DPR don bayar da tata gudnmawar na yaki da yin fasakaurin albarkatun mai a fadin kasar nan.

Acewar Dakta Bictoria Enape, wannan kokarin abin yabawa ne wajen baiwa wajen baiwa fannin mai kula da kuma samar da isasshen man a daukacin fadin kasar nan, musamman gannin yadda ake bin diddigi da ka’ida wajen gudanar da ayyuka a fannin.

Dakta Bictoria Enape tayi nuni da cewar, Nijeriya ta tabka dimbin asarar biliyoyin maira saboda aikata bakalar cin hanci da rashawa da kuma damfara ta hanyar kafar yanar gizo, inda hakan ya janyowa Asusun Gwamnatin Tarayya babbar nakasu.

Shugaba Dakta Bictoria Enape ta sanar da cewar, dole ne aci gaba da yakin da akeyi da cin hanci da rashawa a kasar nan, inda hakan zai sanya Nijeriya ta kara samun ci gaba.

A karshe Dakta Bictoria Enape ta bukaci goyon bayan kamfanin na NNPC don samun gudanar da ayyukanta da kuma ci gaba da bayar da gudunmawar ta na ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: