Connect with us

Da dimi-diminsa

Rikicin APC A Zamfara: Kotu Ta Sa Ranar Yanke Hukunci

Published

on

Kotun koli ta sa ranar 24 ga watan Mayu don yanke hukunci kan rikicin APC na Jihar Zamfara.

Kwamitin Alkalai biyar karkashin jagorancin  Alkalin Alkalan Nijeriya, Ibrahim Tanko Muhammad ne a yau suka sanya wannan rana don yanke hukunci a lamarin.

Bangaren gwamna Yari ne suka daukaka karan bisa hukuncin da kotun daukaka kara ta yi a Jihar Sakkwato, wacce ta tabbatar da matsayar su Sanata Kabir Garba Marafa da ke cewa, ba a yi zaben fid da gwanin APC a Zamfara ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!