Connect with us

LABARAI

Sha’irai Sun Yi Dandazon Addu’ar Marigayi Rabiu Usman A Babban Masallacin Juma’a Na Lokoja

Published

on

Daruruwan al’ummar Musulmi, musamman mambobin kungiyar jama’atul Shu’ara’u reshen Lakwaja da ke jihar Kogi ne su ka hallara a babban masallacin Juma’a na Birnin Lakwaja a ranar Laraba, inda su ka gudanar da sadakar kwanaki bakwai tare da yin addu’oyin tunawa da marigayi shugaban kungiyar ta kasa Zakiru Rabiu Usman Baba na Kano, wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon jiya.

Da ya ke zantawa da wakilin LEADERSHIP A YAU jim kadan bayan kammala addu’o’in, shugaban kungiyar ta Jama’atu Shu’ara’u reshen karamar hukumar lakwaja, Zakiru Dan Musa Muhammed, ya ce, sun shirya addu’oyin ne domin tunawa da shugabansu na kasa, Marigayi Rabiu Usman Baba tare da nema ma sa gafara a wajen Allah (SWT).

Zakiru Dan Musa ya kuma kara da cewa kungiyar ta kadu matuka a lokacin da ta samu labarin rasuwar shugabanta ta kasa,inda ya kara da cewa wagegen gibin da marigayi Rabiu Usman Baba ya bari a duniyar zakarai zai yi wuyan cikewa.

Zakiru Dan Musa kazalika yace shahararren mawakin yabon manzon Allah ya bada gagarumin gudunmawarsa wajen ci gaban darikar tijjaniya da kuma addinin musulunci a Nijeriya dama Afrika ta yamma.Yace marigayi Rabiu Usman Baba ya rera wakoki daban-daban na yabon Manzon Allah da sauran bege na addinin musulunci wadanda za su dade su na tasiri a darikar tijjaniya.

A don haka shugaban kungiyar ta jama’atu Shu’ara’u reshen karamar hukumar lakwajan ya yi addu’ar Allah (SWT) daya gafartawa Marigayi Rabiu Usman Baba tare da kai rahama gare shi da kuma baiwa iyalansa har ma da yayan kungiyar jama’atu Shu’ara’u da ke fadin kasar nan hakurin jure babban rashinsa.

Haka su ma wasu daga cikin mambobin kungiyar a yayin da suke hira da wakilin LEADERSHIP A YAU, sun bayyana alhininsu game da rasuwan Rabiu Usman Baba wanda suka bayyana sa a matsayin babban bango wanda yayiwa darikar tijjaniya da kuma addinin Musulunci hidima a lokacin rayuwarsa.Akan haka suka yi addu’ar Allah ya yafe masa dukkan kura kuransa tare da saka masa da aljannah game da hidimar da ya yi a addinin Musulunci.

A ranan laraban makon jiya ne dai,Allah yayi wa Rabiu Usman Baba Kano rasuwa a birnin Kano,wato garinsa na haifuwa kuma ya rasu yana da shekaru 54 a duniya. Ya rasu ya bar matan aure da yaya da dama.

’Yan Fim Din Kudu Sun Yi Zanga-zanga Kan Kashe-Kashen Zamfara

’Yan wasan fim a karkashin kungiyar ‘Concerned Actors And Seasoned Nollywood Stars’ sun gudanar da zanga-zanga kan kashe-kashen da ke faruwa a Zamfara, da ma sauran wurare a cikin kasar.

Babban dan wasan kwaikwayo, Ejike asiegbu, shi ne ya jagoranci gudanar da zanga-zangar wacce a ka gudanar a jihar Legas. A yayin zanga-zangar, sun koka da irin kashe-kashen da ke faruwa, su na masu kwatanta kashe-kashen da “abun ban tsoro”.

“Bayan lura da abun tashin hankalin da ke faruwa a Zamfara, duba da irin ayukkan da ’yan siyasa ke guidanarwa, mun fahimci cewa, ’yan siyasarmu ne su ka haddasa abun da ke faruwa, su ka sayar da al’ummarsu , wanda hakan ya janyo hasarar dukiyoyi da rayukan al’umma, in ji Asiegbu.

Asiegbu ya kara da cewa, ba za mu sake yin shiru muna kallon ’yan siyasa su na yanda su ka ga dama ba, su na jefa rayukan mutane cikin hadari.

A cewar sa, abin ban mamaki da takaici kan lamarin shi ne, irin yanda ’yan sisayar ke nuna kamar ba su san me ke faruwa ba a fili, alhalin gaskiyar magana, kowa ma ya san cewa, su ne ke da hannu a dukkan abubuwan da ke faruwa na kashe mutanen da basu-ji-basu-gani ba saboda cimma muradansu na son rai.

Asiegbu ya zargi ’yan siyasar da juya wa al’ummarsu baya; su din da su ka yi alkawarin kare rayukansu da dukiyoyinsu. Mun ji cewa zinare na da kima da daraja, to amma ya za a kwatanta shi da rayuwa? Sayar da rayuka al’umma a madadin zinare da gwal mugun abu ne da kowane dan Najeriya yakamata ya yi Allah-wadai akai domin samar da zaman lafiya a yankin.

“Su wadannan ‘’yan siyasar ba aljannu ba ne ko boyayyu, a cikin al’umma su ke rayuwa; an san su, akwai ma su daukar nauyin su. To amma su gane, sum adin, za a iya wayuwar gari, wadannan da ke saka su su na yin abunda su ke yi, su jiya masu baya, su sa a kashe su,” In ji Asiegbu a wurin Zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, idan dai har ba an dauki matakan da su ka dace ba cikin gaggawa kan lamarin, to ba za a taba samun sauki kan lamarin ba, musamman duba ga irin yanda ma su hannu a kan kashe-kashen su ka zaku da abin.

Daga karshe, masu zanga-zangar sun shelanta cewa, zinare da gwal din da ke Zamfara ban a mutum daya ne ko na wasu ‘yan tsiraru, a’a, kamar yanda man fetur din da ke Nija-Delta yak e na dukkan ‘’yan Najeriya, to haka shi ma zinare da gwal din Zamfara, na kowa da kowa ne.

Zanga-zangar dai ta samu halartar manyan ’yan fim kamar irin su; Paul Obazele, Sonny McDon, Emeka Ossai, da kuma wasu masu shirya fim da su ka hada da; Chico Ejiro, Zeb Ejiro, Tony Ani, Mike Niam da wasu sauran mahalarta.

’Yan Sanda Sun Damke Mutane Uku Kan Zargin Lalata ’Yar Shekara 10 A Hunkuyi

Hukumar ‘Yan sanda sun damke wasu mutane da zargin bata wata yarinya yar shekaru 10 a garin Hunkuyi da ke karamar hukumar Kudan ta jihar kaduna.

Wakilinmu ya ziyarci garin don jin yadda lamarin ya wakana. Malam Adamu Sambo shi ne kakan yarinyar da a ke zargin mutanen sun bata, kuma shi ya yi magana a madadin uban yarinyar mai suna Lariya Sambo.

Da farko dai Malam Adamu Sambo ya shaida wa manema labarai cewa, a ranar 5 ga Mayu, 2019, ne jama’ar unguwar Fulani da ke cikin garin Hunkuyi su ka tsare wani dattijo a yayin da su ka gan shi da jikansa mai suna Lariya tare da tuhumar sa dalilin ganin su tare a matsayinsa na dattijo. Hakan ya sa idon dattijo ya yi jajir daga bisani ya ranta a na kare.

Bisa haka ne jama’ar garin suka ba iyayen yarinyar shawara da cewa a tuhumi yarinyar a kan lamarin. Malam Sambo ya aminta da shawarar jama’ar gari kuma take ya tuhumi yarinyar cikin siyasa a kan mene ne tsakaninsu da wancan dattijo sai yariya ta kada baki ta ce, “su na kira na ne wani daki suna kwantar da ni.”

Jin wannan kalmar ce Malam Sambo ya kai kukansa ofishin ’yan banga na garin Hunkuyi don binciken lamarin.

Bayan an gayyato dukkan wadanda Lariya ta ambata sun kai ta dakuna sun kwanta da ita, sai ’yan bangan su ka gayyato dukkan wanda yarinya ta zayyana sunansu a wannan ofishin na ’yan bangar.

Daga cikin wadanda yariya ta ambata akwai Malam Shagari da Malam Yahaya da Malam Sadiku.

Bayan tambayoyi da ’yan banga su ka yi wa wadanda a ke zargin, hakan ya sa dole sai da a ka dangana da babban asibitin da ke garin Hunkuyi, don yiwa yarinya gwaji.

Kamar yadda suka sami sakamakon gwajin ne yasa lamarin ya koma wajan hukumar yan sanda na garin hukuyin don tsare wadanda ake zargi a cikin lamarin.

Ofishin ’yan sanda da ke lura da karamar hukumar Kudan bakidaya da ta gama nata binciken ne sai ta dauki wadanda a ke zargin zuwa helkwatan ’yan sanda na jihar Kaduna don cigaba da binciken lamarin.

Wakilinmu ya garzaya ofishin binciken manyan laifuka na kasa reshen jihar ta Kaduna, don jin ko ya lamarin ya kaya, amma dai sai manyan jami’an gurin su ka ce ba su da hurumin cewa uffan a kan lamarin.

Wakilinmu namu bai kasa a gwiwa ba sai ya niki gari zuwa wajen kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Ado, don jin ko me zai ce a kan mutanen da a ke zargi da lalata wata yarinya ’yar shakara 10 daga garin Hunkuyi? Nan take ya daga waya ya tuntubi sashen binciken manyan laifuka, don su gaya ma sa inda a ka kwana.

DSP Yakubu ya tabbatar da cewa wadanda a ke zargin su na hannun ’yan sanda a na cigaba da binciken lamarin, amma da zarar  sun gama za su tura su kotu don yi mu su hukunci.

Wannan lamari ya ja hankalin mutanen karamar hukumar musamman yadda labarin ke yawo a cewa wadanda a ke zargin za su yi iyakar yinsu wajen kubutowa daga inda su ke duk da irin rashin goyan baya da ba su samu ba a bangaren manyan gari da sauran masu fada-a-ji a karamar hukumar.

Bisa haka ne shugaban karamar hukumar ta Kudan, Hon. Shu’aibu Bawa Jaja ya yi kira ga jama’a da su bai wa jami’an tsaro goyan baya wajen kai masu rahoton duk wani batagari, don samun zamn lafiya mai dorewa a karamar hukumar tasa da jihar kaduna baki daya. Kuma ya ja hankalin iyaye da su kula da tarbiyar yaransu a koda yaushe.

Ya zuwa hada wannan labarun dai jama’ar gari da kungijoyin kare hakin bil Adama da kafafen yada labarune suka zura idanu akan lamarin don ganin an tabbatar da adalci akan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!