Connect with us

MAKALAR YAU

Tsoho Donald Trump, Buhari Da Ganduje

Published

on

Mutane za su yi mamakin ganin sunayen Trump, Buhari da Ganduje tare da tambayar menene ya hana wadannan mutane? Na farko dai dukkansu sun kai shekaru 70 a duniya; shekarar da Majalisar Dinkin Duniya ta saka a matsayin duk wanda ya kai ta ya cika tsoho. Wani abin kuma da ya hada wadannan mutane shi ne kasancewar dukkansu na da karfin iko na mulki a tsarin siyasa, domin Tump ya kasance shugaban kasa mafi karfin iko a duniya, shi kuma Buhari mafi karfin iko a nahiyar Afirka, yayin da Ganduje ta karfin tsiya ya zama gwamna mafi karfin iko a gwamnonin Najeriya.

Duk da cewa babu wani bincike na kimiyya da ya tabbatar da cewa tsofaffi ’yan sama da shekaru 70 ba za su iya yin harkokin mulki ba, amma dai bincike ya tabbatar da cewa yawancin ’yan sama da shekaru 70 na fuskantar matsaloli kama daga rashin sauri da kuzari na jiki da kwakwalwa, rauni, ciwon kunne da karancin gani, kafiya wajen bin abinda a ka saba da shi, raguwar kaifin basira da kuma ciwon mantuwa. Bincike na game da wadannan shugabanni guda uku ya nuna min cewa dukkansu na fama da wasu daga cikin wadancan larurori da ke da alaka da tsufa.

Idan mu ka dauki Donald Trump, a bayyane ya ke cewa Amurka ba ta taba samun shugaba wanda ya zamar ma ta abin kunya a idon duniya kamar sa ba, saboda sakarcinsa. Ga abinda wani Ba’amurke, Mick Lake na jami’ar Wesleyan da ke Indiyana ke cewa game da shugaban nasu; “…ba maganar siyasa ba, Trump sakarai ne. Magana ce ta gaskiya. Shugabannin duniya sun raina shi yadda hatta shugabannin Afirka ke ma sa dariya a bainar jama’a. Abu guda da za ka ce Trump ya yi na a-zo-a-gani shine fitowa ta tsatson babansa Fred Trump, wanda ya mutu ya bar masa gadon kudi Dala miliyan $500.”

Mun ga yadda Trump ya jawo tsayawar aikin gwamnatin Amurka na tsawon makonni wanda ya hana ma’aikata dubu 800 samun albashi da asarar biliyoyin daloli ga gwamnatin Amurka, amma duk a banza.

Idan mu ka dawo Afirka, kamar yadda na fada a baya, majalisar dinkin duniya ta ayyana shekarun tsufa sun fara ne daga shekara 65, amma mu a nan Afirka saboda wasu dalilai na gazawa sai a ka yanke cewa shekarun tsufan mu ya fara daga shekara 55 ne. Shugaba Buhari ya yi murnar cika shekaru 76 kwanakin baya, duk da cewa yawancin mutanen Arewa, daga lokacin mulkin mallaka zuwa bayansa ba mu da cikakken tsari na ajiye bayanai na haihuwa.

Yawancin mutane na amfani da kiyasi wajen bada shekarunsu wanda yawanci kuma ya na gaza ainihin shekarunsu na gaskiya. Sunan da a ka fi kiran Buhari tun dawowarsa mulki karo na biyu shi ne Baba Go-slow, wato mai tafiya sannu-sannu, wanda bai rasa nasaba da shekarunsa. Sannan mun ga yadda ya yi ta fama da ciwon kunne tsawon watanni. A lokacin hirarsu da Kadaria Ahmed kafin a yi zabe, mun ga yadda sai da Osinbajo ya yi ta kawo ma sa dauki wajen amsa wasu tambayoyi, sakamakon kasa fahimta cikin gaggawa ko kasa ji. Ciwon mantuwa ya bayyana tare da Buhari musamman lokacin da ya ke yawon yakin neman zabe, inda ya ke manta mutane ko wurare.

Duk da ya ci zabe a karo na biyu, amma dai kasar a sannu-sannu abubuwa na ta tabarbarewa kuma al’amura na da ban tsoro domin tamkar ya gagara aikinsa yadda ya kamata. Abu guda tun bayan cin zabe na a-zo-a-gani da Buhari ya yi shi ne na samun ceto yarinya Zainab Aliyu, wadda hukumomin Saudiyya su ka caza da safarar miyagun kwayoyi. Shi ma sai da kafafen sadarwa su ka yi ca sannan ya motsa, kuma cikin awa 24 da saka bakinsa a ka saki yarinyar.

Akwai yanayin halin hadarin da kasar ke ciki na bukatar Buhari ya yi murabus ya baiwa mataimakinsa mulki ko abubuwa za su motsa. Sauka daga mulki a wannan gaba zai taimaki ita kanta jam’iyyar APC a shekarar 2023 su sami damar cin zabe, saboda dole su tsayar da Osibanjo, amma matukar Buhari ne a a ka yi zaben cikin gida na dan takarar shugaban kasa hakan zai iya yaga jam’iyyar, abinda zai ba wa PDP nasara. Magana ta gaskiya Buhari ya gaza a yanzu kuma idan a ka cigaba a haka hadarin da kasar ke ciki, musamman yankin Arewa maso Yamma sai abinda Allah ya yi. Kada a manta, da ma dai tuni yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

A matsayin wanda ya yi fice sakamakon yaki da cin hanci, akwai daure kai yadda ko sau daya Buhari bai taba fitowa fili ya la’anci zargin cin hanci da a ka yi wa Ganduje ba, sai ma kokarin yi wa abin kwaskwarima. Sannan Buhari ya zura ido yadda ’yan barandan APC su ka dakile zaben gwamna na Kano tare da kwace kujerar da karfin tsiya. Amma mun ga yadda Buharin ya tsaya tsayin daka wajen ganin nasa zaben ya yi nasara, domin ya bada umarnin a harbi duk wani barawon akwati, abinda ya jawo a ka yi zaben shugaban kasa mafi tsafta a tarihin kasar nan.

Tsoho na karshe shi ne Ganduje, dan shekaru 70 wanda ba ya jin kunyar Allah balle ta jama’a. Duk da bin kazamar hanya wajen kwace zabe a Kano, maimakon ya koma ga Allah ya nuna shukurar sake zama gwamna ta hanyar kwantar da hankalin samarin da su ka ki jefa masa kuri’a, sannan ya yafewa ’yan adawarsa, ya hada kan kowa domin kawo cigaba a jihar, sai ga shi ya zama kamar wani mahaukacin kare.

Da alama dai ciwon tsufa “senility” ya kama shi. Ya na bin hanyoyin da sai ya ruguza masauratar Kano da sarkinta. Ya yi amfani da ’yan barandansa da ke majalisa wajen yin kudurin kacaccala masarautar, abinda ba zai haifar wa jihar da mai ido ba sakamakon karin kudaden kashewa da gwamnatin za ta almubazzarantar a masauratun a halin da yara ba su iya biyan kudaden makaranta kuma jama’a ke bukatar ruwan sha da ayyukan yi. ’Yan majalisa sun biye wa tsohon duk da cewa, kotu da ya garzaya a lokacin badakalar dala wajen ceto kansa, a yanzu ita ya yi wa karan tsaye duk da cewa ta dakatar da shi wajen ci gaba da rantsar da sabbin sarakunan. Ya ilahi idan mahukunta za su riki amfani da kotu su kare kansu daga ta’asa da su ka dibga sannan su yi biris da ita lokacin da ta taka musu birki, ina al’umma zata dosa?

Arewa maso yamma na fuskantar kalubalen da ba ta taba fuskanta ba na masu kai hari da satar mutane amma abin takaici ko’ina a kafafen sada zumunta ba wani abu da ake Magana sai rigimar Ganduje da Sunusi. Cikinsu ba wanda zai tada jijiyar wuya wajen kare talaka amma sai ga shi talakawa na ta yaki a kansu. Shi Sarki Sunusi, shi ya jawa kansa halin da ya ke ciki, domin dai ya gaza wajen ganin ya tattaro manyan jihar Kano waje guda domin samarwa da jihar mafita daga halin da ta ke ciki. Abinda ya dame shi shine kawai ya yi ta babatu a jaridu da taruka domin a tafa masa, ba tare da wani abin azo-a-gani da ya kafa ko jagoranta a kasa ba. Da ya hada kan mutanensa sun zama murya guda da ke nemo yancin mutanenta da wallahi Ganduje bai isa ya yi masa wannan wulakanci ba. A matsayinsa na hamshakin attajiri mai ilimi, ka taba jin wata gidauniya ta sa ta tallafawa ilimi? Ga sa’o’insa nan irinsu Tony Emelu wanda ke da gidauniya da ke tallafawa matasa a fadin kasar da tallafin karatu da na jari. A yanzu haka hukumar cin hanci da rashawa na da takardu da su ka shirya wajen ganin sun gurfanar da Sarkin a gaban kotu bisa zargin badakala a masarauta.

Wajibi yan arewa mu tashi tsaye kuma mu gane cewa shugabannin da mu ke da su a yanzu wallahi ba za su taimake mu ba wajen yakar jahilci da talauci. Kuma matukar ba mu yaki wadannan munanan yan tagwaye ba wallahi sai sun murkushe mu, kuma kowa ya ga ni cewa an kama hanya. Duk wata jiha a arewa daidai ta ke da zama Zamfara idan ba’a samarwa da matasanmu ilimi da aikin yi ba. Kuma idan akwai wani shugaba da zai iya kawo canji a bayan Buhari ya ke, amma Buhari ya gaza. Da wahala mu sake samun wani shugaba a kasar nan wanda zai iya samun goyon baya da yarda irin wadda Buhari ya samu. Domin a tarihi Buhari ne kadai ya taba kara kudaden albarkatun man fetur amma talakawa bas u yi masa zanga-zanga ba. Kuma daga Akwa Ibom zuwa Akwanga, daga Birnin Kebbi zuwa Bini daga Lafia zuwa Lagos kai hatta kasar inyamurai wadanda ba sa boye kiyayyarsu ga Buhari, mun ga yadda aka rika dafifi da ruwan kuri’u ga Buhari har ya sake dare miulki a karo na biyu. Amma abin takaici tsohon ya gaza fidda A’i daga rogo, shin tsufa ne ko mantuwa ya kawo wannan gazawa? Ko ma menene, lokaci ya yi da zamu daina mika ragamar mulkinmu ga tsofaffi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!