Connect with us

LABARAI

Tsohon Ministan Nijeriya Ya Bayyana Muhimmancin Kimiyya Da Fasaha

Published

on

Tsohon Ministan samar da wutar lantarki, Farfesa Chinedu Nebo a jiya Laraba ya bayyana muhimmancin kimiyya da fasaha. Inda ya ce; inda ya ce idan har ba a bai wa bangaren kimiyya da fasaha muhimmanci ba ta hanyar zuba hannun jari da ganin ci gaban bangaren ba, to babu yadda za a yi tattalin arzikin irin wannan kasa ya bunkasa.

Farfesa Nebo ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da jawabi a taron kwanaki uku da aka shirya na ‘Biennial Engineering Conference’ da tsangayar kimiyya da fasaha da jami’ar gwamnatin tarayya ta Alex Ekwueme (AE-FUNAI) dake Ndufu-Alike, Ikwo, a jihar Ebonyi ta shirya.

Taron wanda ya samu halartar zakakurai kuma masana daga jami’o’i, ma’aikatu da kuma masana a bangarori daban-daban na kimiyya da fasaha. Taron an yi masa take da; “Engineering and Technology: A Driver for Sustainable Development’’ wato amfani da bangaren kimiyya da Fasaha wajen samar da ci gaba.’

A cewarsa Nijeriya na da bukatar ta tashi tsaye wajen bai wa bangaren kimiyya da fasaha muhimmanci domin bunkasa tattalin arzikinta. Ya ce; hatta a bangaren ma’aikatu akwai bukatar amfani da kimiyya da fasaha wajen yiwa bangaren kwaskwarima domin samar da wadansu kayayyakin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!