Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Damke Mutane Uku Kan Zargin Lalata ’Yar Shekara 10 A Hunkuyi

Published

on

Hukumar ‘Yan sanda sun damke wasu mutane da zargin bata wata yarinya yar shekaru 10 a garin Hunkuyi da ke karamar hukumar Kudan ta jihar kaduna.
Wakilinmu ya ziyarci garin don jin yadda lamarin ya wakana. Malam Adamu Sambo shi ne kakan yarinyar da a ke zargin mutanen sun bata, kuma shi ya yi magana a madadin uban yarinyar mai suna Lariya Sambo.
Da farko dai Malam Adamu Sambo ya shaida wa manema labarai cewa, a ranar 5 ga Mayu, 2019, ne jama’ar unguwar Fulani da ke cikin garin Hunkuyi su ka tsare wani dattijo a yayin da su ka gan shi da jikansa mai suna Lariya tare da tuhumar sa dalilin ganin su tare a matsayinsa na dattijo. Hakan ya sa idon dattijo ya yi jajir daga bisani ya ranta a na kare.
Bisa haka ne jama’ar garin suka ba iyayen yarinyar shawara da cewa a tuhumi yarinyar a kan lamarin. Malam Sambo ya aminta da shawarar jama’ar gari kuma take ya tuhumi yarinyar cikin siyasa a kan mene ne tsakaninsu da wancan dattijo sai yariya ta kada baki ta ce, “su na kira na ne wani daki suna kwantar da ni.”
Jin wannan kalmar ce Malam Sambo ya kai kukansa ofishin ’yan banga na garin Hunkuyi don binciken lamarin.
Bayan an gayyato dukkan wadanda Lariya ta ambata sun kai ta dakuna sun kwanta da ita, sai ’yan bangan su ka gayyato dukkan wanda yarinya ta zayyana sunansu a wannan ofishin na ’yan bangar.
Daga cikin wadanda yariya ta ambata akwai Malam Shagari da Malam Yahaya da Malam Sadiku.
Bayan tambayoyi da ’yan banga su ka yi wa wadanda a ke zargin, hakan ya sa dole sai da a ka dangana da babban asibitin da ke garin Hunkuyi, don yiwa yarinya gwaji.
Kamar yadda suka sami sakamakon gwajin ne yasa lamarin ya koma wajan hukumar yan sanda na garin hukuyin don tsare wadanda ake zargi a cikin lamarin.
Ofishin ’yan sanda da ke lura da karamar hukumar Kudan bakidaya da ta gama nata binciken ne sai ta dauki wadanda a ke zargin zuwa helkwatan ’yan sanda na jihar Kaduna don cigaba da binciken lamarin.
Wakilinmu ya garzaya ofishin binciken manyan laifuka na kasa reshen jihar ta Kaduna, don jin ko ya lamarin ya kaya, amma dai sai manyan jami’an gurin su ka ce ba su da hurumin cewa uffan a kan lamarin.
Wakilinmu namu bai kasa a gwiwa ba sai ya niki gari zuwa wajen kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Ado, don jin ko me zai ce a kan mutanen da a ke zargi da lalata wata yarinya ’yar shakara 10 daga garin Hunkuyi? Nan take ya daga waya ya tuntubi sashen binciken manyan laifuka, don su gaya ma sa inda a ka kwana.
DSP Yakubu ya tabbatar da cewa wadanda a ke zargin su na hannun ’yan sanda a na cigaba da binciken lamarin, amma da zarar sun gama za su tura su kotu don yi mu su hukunci.
Wannan lamari ya ja hankalin mutanen karamar hukumar musamman yadda labarin ke yawo a cewa wadanda a ke zargin za su yi iyakar yinsu wajen kubutowa daga inda su ke duk da irin rashin goyan baya da ba su samu ba a bangaren manyan gari da sauran masu fada-a-ji a karamar hukumar.
Bisa haka ne shugaban karamar hukumar ta Kudan, Hon. Shu’aibu Bawa Jaja ya yi kira ga jama’a da su bai wa jami’an tsaro goyan baya wajen kai masu rahoton duk wani batagari, don samun zamn lafiya mai dorewa a karamar hukumar tasa da jihar kaduna baki daya. Kuma ya ja hankalin iyaye da su kula da tarbiyar yaransu a koda yaushe.
Ya zuwa hada wannan labarun dai jama’ar gari da kungijoyin kare hakin bil Adama da kafafen yada labarune suka zura idanu akan lamarin don ganin an tabbatar da adalci akan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: