Connect with us

LABARAI

Yanzu Kowa Zai Iya Duba Sakamakon Jarabawarsa A Shafinmu- Hukumar JAMB

Published

on

Hukumar da ake shirya jarabawar sharen fagen shiga jami’a wato JAMB ta bayyana cewa; yanzu kowanne dalibi da ya rubuta jarabawar yana da damar duba sakamakon jarabawar na su a babban shafin hukumar. Dk. Fabian Benjamin, shugaban sashen hulda da kafafen watsa labarai na hukumar, shi ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a yayin zantawarsa da manema labarai a garin Legas.

A cewarsa ya zuwa hada wannan rahoton akalla dalibai miliyan 1.5 ne suka duba sakamakon jarabawarsa zuwa yanzu ta hanyar amfani da lambarnan ta 55019. Ya ce; a don haka yanzu tuni hukumar ta fara sanya sakamakon jarabawar a shafinta, inda ya ce yanzu daliban na da damar su hau shafin domin bincika sakamakon jarabawarsu domin su fitar da ita. Mai magana da yawun hukumar ya yi watsi da zargin cewa lambar 55019 ba ya aiki.

Idan ba ku manta ba a ranar 11 ga watan Mayu hukumar JAMB din ta bayyana cewa ta saki sakamakon jarabawar. Rahotanni sun nuna cewa; akalla mutum miliyan 1.8 ne suka rubuta jarabawar ta bana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!