Connect with us

Da dimi-diminsa

DSS Ta Saki Ustaz Idris Abdul’aziz Da Ke Bauchi

Published

on

Jami’an tsaron farin kaya ta (DSS) ta sallami Ustas Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi daga tsarewar da ta masa domin ya amsa mata tambayoyi.

Ustas Dutsen Tanshi dai shine babban Limamin Massalacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, ya shiga hanun DSS din ne tun ranar Juma’ar da ta gabata.

Da yake tabbatar da sako Malamin nasu, daya daga cikin mambobin Majalisar Koli ta Daliban Malam Idris, Muhammad Abdulkadir ya tabbatar wa LEADERSHIP A YAU sake Malamin da aka yi.

Ya ke cewa; “Eh tabbas sun sako Malam yanzu haka yana tare da ‘yan uwa. Alhamudllahi, wannan jarabawace wacce tana iya shafan kowani Malam muddin ya tsaya kan gaskiya.

“Daman haka hanyar take, wannan koyi ne daga rayuwar Annabawa,” A cewar shi.

Ya ce, wannan kamun da aka yi wa Malaminsu zai kara masa daukake ne ma a idon duniya ba kuma tauye masa kimarsa ba.

Muhammad Abdulkadir ya shaida cewar kawo yanzu dai ba su da wani masaniya kan cewar ko DSS din sun gindaya wa Malaminsu wasu sharuda, ya dai tabbatar da cewar an sako shi kuma ya dawo cikin iyalansa lafiya ba tare da wani matsala ba.

Wakilinmu ya nakalto cewar DSS sun cafke Malam Idris ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sai dai babu wani da zai iya bayyana hakikanin dalilin cafkewar da suka masa, dalibansa dai sun ce tambayoyi ne kawai DSS din suka yi wa Malamin nasu.

Cikakken labarin na tare.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: