Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

CITAD Ta Yi Tir Da Soke Dokar Kwato Dukiyar Talakawa Da Barayin Gwamnati Suka Sace A Bauchi

Published

on

  •  Cibiyar Ta Gargadi Gwamnan Jihar Da Kada Ya Kuskura Ya Sanya Hanu

Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa (CITAD) a takaice, ta yi tir da matakin da Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta dauka na soke dokar kwato dukiya da kadarorin al’umma da ma’aikata suka sace a lokacin da suke bukunan aiyukansu.

Cibiyar wacce kungiya ce mai zaman kanta, ta kuma jawo hankalin gwamnan jihar Bauchi da cewar kul ya sanya hanu kan wannan dokar domin a cewar cibiyar babu alfanun da sokewar zai yi wa jama’an jihar, illa baiwa barayin gwamnati mafaka wanda kuma a cewarsu hakan bai dace ba ko kadan.

Babban Jami’in Shirye-shirye na kungiyar ta CITAD, Mohammed Chiroma Hassan, shine ya yi wannan sukar a wani taron manema labaru da ya kira jiya Juma’a a ofishinsu da ke Bauchi, yana mai karawa da cewa ko kadan soke dokar ba zai ciyar da jihar gaba ba, ya kuma kara da cewa soke dokar da majalisar ta yi da kanta koma baya ne ga ci gaba matuka.

Idan za ku iya tunawa dai kamar yadda muka kawo muku labarin da ke cewa a ranar Laraba ne majalisar dokokin jihar Bauchi ta soke dokar kwatowa da kuma tuhumar barayin gwamnati a bisa kudi ko kadarorin da suka wawushe na jama’a. dokar ta samu suka daga bangarori daban-daban na jama’an jihar a bisa haka ne ma CITAD ta nuna bacin ranta kan dokar.   

Mohammed Chiroma yake cewa; “Cibiyar CITAD ta riski labara cike da ban mamaki da takaici na daukar matsayar da majalisar dokokin jihar Bauchi ta yi na soke dokar bincike, tuhuma da kuma kwato dukiyar jama’a da wasu suka wawushe. Soke wannan dokar da suka yi a shekarar 2017 ba zai taimaki al’ummar jihar ko kadan ba, illa dai zai baiwa barayin dukiyar talakawa kariya, wanda kuma jama’a ba za su yi farin ciki da hakan ba.

“Ita wannan gwamnatin ita ce ta kawo wannan dokar da zai tabbatar da bincike ko kwato dukiya ko kadarorin gwamnati da ma’aikata suka sata a shekarar 2017 aka yi dokar. Don haka ba daidai ba ne soke wannan dokar a daidai wannan bigiren da jama’a suke gayar bukatar irin wannan dokar,” A cewar cibiyar.

Chiroma ya daurawa da cewa; “Muna zargin an samar da wannan dokar a fari, a dawo kuma yanzu a soke wannan dokar a matsayin wata hanya kawai ta nema wa gwamnati bai barin gado kariya daga dukkanin bincike ko tuhumar yadda ta tafiyar da dukiyar jama’an jihar, wanda hakan ba zai faranta wa al’ummar jihar rai ba,” A cewar shi.

Cibiyar ta yi zargin cewar hatta yadda ‘yan majalisun suka bi wajen amincewa da wannan dokar da yi masa karatu na daya zuwa na uku a lokaci daya a matsayin wata tsararriyar lamari, “Hatta zaman da majalisar ta yi a ranar 15 ga Mayun 2019 ba su shiga zaman a lokacin da suka saba ba. Sannan ‘yan majalisu 13 ne kadai suka hallara a cikin ‘yan majalisu 31 na jihar, wannan akwai abun dubawa da zargin kawai nema wa gwamnati mai barin gado kariya daga kowace irin tuhuma ne,” A cewar CITAD.

Muhammad Chiroma Hassan ya kuma kara da cewa, cibiyarsu ta tabbatar da cewar dukkanin wani abu mai sarkakiya da gayar muhimmanci a cikin al’umma akwai gayar bukatar a bude tattaunawar jin ra’ayin jama’a kan batu kafin zuwa ga aiwatar da shi a matsayin doka, sai ya nuna cewar wannan ba shine jama’a suke so ba, “Kawai neman kariyan kai ne, amma ya dace a jiwo ra’ayin jama’a kafin a fara kokarin soke wannan dokar,” Kamar yadda suka shaida.

Daga bisani Cibiyar ta fitar da matsayarta kwarara guda uku da take son a tabbatar da cimmasu, “Dukkanin wani lamari mai cike da sarkariya ga jama’a wanda ka iya shafan rayuka da tattalin arzikin jama’an jiha to lallai akwai gayar bukatar tuntubar jama’an gabanin daukar mataki kan wannan babin. Muna son a yi kan wannan ma.

“A saninmu da gwamnan jihar wanda masani ne kan shari’a da doka mun tabbatar yana sane da dukkanin wata kalubalen da ke tattare da soke doka, don haka muna kiransa da ya tabbatar da kare martabar doka ta hanyar kin sanya hanu kan wannan dokar,” A cewar su.

Kana sun kuma shaida cewar dole ne a maido da kudurin ga jama’an jihar Bauchi gabanin aiwatar da wani abu domin tabbatar da adalci a tsakanin al’umman jihar a matsayin abun da suke nema na uku.

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa ta kuma bayyana matsayarta da cewar tana sukar matakin, “Muna tir da wannan dokar, kana muna kira ga dukkanin wadanda abun ya shafa da masu ruwa da tsaki a jihar nan da su tabbatar da yin watsi da wannan kudurin domin ci gaban al’umman jihar Bauchi,” A cewar CITAD.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!