Connect with us

KASUWANCI

Ayyukan Masu Sace Mutane A Arewa Zai Janyo Karancin Abinci, Cewar Manoma

Published

on

Wasu manoma a Arewacin Najeriya sun yi gargadin cewar, ayyukan masu sace mutane musamman a jihohin Katsina da Zamfara da kuma sauran jihohin da ke cikin kasar, zai iya janyo karancin abinci a daukacin fadin kasar nan.

Har ila yau, manoman sun kuma koka akan rasa wasu yan uwansu manoma da  masu garkuwa da mutane su ka sace, musamman a jihar Katsina da jihar Zamfara, inda suke yi nuni da cewar, daga watan Janairu zuwa watan Afirilu kadai an kasha maoma da dama a cikin gonakan su.

Manoman sun sanar da hakan ne a hirarsu daban-daban  da jaridar Thisday a satin da ya gabata, inda su ka ce tabbas Nijeriya zata fuskanci karancin abici saboda ta’addacin masu yin garkuwa da mutane.

Bugu da karai, manoman sun bayyana cewar, baya ga karancin abinci da ayyukan na ta’addancin masu garkuwar zai hairfar, hakan kuma zai yiwa tattalin arzikin kasar nan nakasu.

Daya daga cikin manoman dake a karamar hukumar Batsari  cikin jihar Katsina Bala Halisu ya sanar da cewar, ayyukan masu yin garkuware a jihohin dake Arewacin Nijeriya ya shafi yin noma a yankin, inda ya yi nuni da cewar, manoma da dama suna jin tsoron shiga gonakansu don gudanar da aiki.

A cewarsa, ya kamata ne ace a yanzu moman dake a jihar Katsina sun fara shirin yin noman bana, amma a yanzu hakan mafi yawancin sun arce yin gudun hijira a gidajen yan uwan su dake a cikin birane don tsira da rayuwakan su da kuma ta iyalansu a saboda haka bamu san yaush e zamu koma gidajen mu ba don fara yin noma ba.

Halisu ya yi kira ga Gwmnatin Tarayya da basu kariyar rayuwar su da kuma dukiyoyin su, inda yace, in har ba’a Gwamnatin Tarayya data jihohi basu  dauki matakan da suka dace ba, tabbas za a fuskanci karancin abinci a kasar nan, inda hakan zai janyo yin yunwa a kasar nan.

Shi ma wani manomin Shinkafa a karamar hukumar  Safana a cikin jihar Alhaji Aliyu Babangida Maishinkafa ya sanar da cewar, za’a fuskanci matsanincin karancin abinci a kasar nan, ganin cewar, ayyukan masu sace motane ya hana manoman zuwa gonakan su don gudanar da aiki.

A cewar Maishinkafa, tabbasa za’a fuskanci karancin abinci a kasar nan, saboda maoman basa iya shiga gonakan su, sakamakon ayyukan na masu sace mutane.

Ya kara da cewa, za’a samu karancin gudanar da ayyukan noma a manyan yankunan dake Arewacin kasar nan kuma za’a samu karancin abinci a a karashen shekarar 2019, inda ya yi nuni da cewar, an kashe manoma da dama an kuma tarwatsa mazaunin su tare da asarar dukiyoyin su.

Ya sanar da cewar, ayyukan na masu sace mutane sai kara karuwa yake yi a kullum kuma ayyukan nasu sai kara tabarbarar da tattalin arzikn yankin na Arewa yake yi.

Shi kuwa, wani masanain tattalin arzikin kasa  dake a sashen koyon darasin tsimi da tanadi a jimi’ar Umaru Musa Yar’Adua dake a jihar Katsina ya koka akan yadda lamarin na masu sace mutane, musaman a jihar yake kara zamowa rowan dare, inda yace hakan yana yiwa tattalin arzikin jihar nakasu.

Malamin yaci gaba da cewa, mafi yawancin maoman basa iya zuwa gonakan su saboda tsaoron kada a sace su, inda ya yi nuni da cewar, hakan zai janyo mummunan karacin abinci a a kasar nan, musaman a Arewacin kasar nan.

Ya kara da cewa, hakan zai kuma janyo talauci da kara yawan rashin ayyukan y da kuma shafar tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.

Malamin ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya  data gaggauta magance rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa da kuma kara daukaka huddar yansanda da alummar gari yadda za’a magance ayyukan masu sace mutanen  da kaucewa tabarbarewar rashin tsaro.

Shima a nasa bayanin, Shugaban masu noma Shinkafa ta kasa AFAN reshen jihar Katsina State, Alhaji Umar Ya’u,ya koka akan yadda ayyukan na masu sace mutane yake janyowa monoman jihar matsala.

A cewar Shugaban masu noma Shinkafa ta kasa AFAN reshen jihar Katsina State, Alhaji Umar Ya’u, ayyukan na masu sace mutane ya janyo mamoma da dama sun arce daga gidajen su, inda ya yi nuni da cewar, hakan zai janyo karancin abinci musamman a Arewacin Nijeriya.

Shugaban masu noma Shinkafa ta kasa AFAN reshen jihar Katsina State, Alhaji Umar Ya’u, ya sanar da cewar, wasu moman sun yi watsi da yin noman kwata-kwata saboda tsoron masu sace mutane, inda wasun suka sake gari.

Shugaban masu noma Shinkafa ta kasa AFAN reshen jihar Katsina State, Alhaji Umar Ya’u,  yace, in har ba’a dauki matakan da suka dace ba daukacin al’amuran noma a jihar Katsina za su tsaya tsakiya.

Alhaji Umar Ya’u  ya yi kira ga Gwamnatin Trayya da gwamnatocin jihohi dasu dauki matakan da suka dace don kawo karshe ayyukan na masu sace mutane, musamna  don gudun jifa a kasar na  acikin fairi.

A wata sabuwa kuwa, Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu ya amince da cewar, jihar ta katsiana tana fama da kalubalen rashin tsaro, musamman a wasu kananan hukumomi da wasu kauyukan dake cikin jiha

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu ya kuma bayar da tabbacin cewar gwamnatin jihar zata yidukkan mai yiwa don magance ayyukan na masu sace mutane

Acewar Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu wanda ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyara a ma’aikatar noma ta jihar zata samar da mafita don baiwa manoman kariya yadda zasu samu suknin komawa gonan ku su da kuma magance kalubalen da manoman suke fuskata.

Ya kara da cewar, gwamnatin jihar zata kuma bayar dukan tsaron da ake bukata ga hukumomin aikin noma dake jihar don magance su daga shiga kalubalen rashin tsaro.

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu  ya kuma shawarci manoman kada su ji tsoro akan ayyukan da masu sace mutanen suke aikawa, domin Gwamnatin Trayya data jihar suna yin iya kokarin su don kawo karashen lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!