Connect with us

MANYAN LABARAI

Bashin Gwamnati Mai Ruwa Ba Haramun Ba Ne A Musulunci – Sheikh Khalil

Published

on

An bayyana cewa, Musulunci bai haramta irin bashin da gwamnati ke bayarwa mai ruwa ta hannun manyan bankunanta da kuma bankunan kasuwanci ba.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta kasa reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, a tattaunawarsa da wakilin LEADERSHIP A YAU a Kano kwanaki kadan da kammala taron kungiyar bunkasa jihar Kano, wato KCCI.

Shehin malamin ya yi karin haske da cewa, babban dalilin da ya sa wasu malamai ke haramta cin irin wannan bashin shi ne, rashin fahimtar yadda ya ke da kuma yanayin asalinsa da tasarifinsa, alhali tuni manyan wayayyun malamai a kasashen duniya su ka bayar da fatawar da ta bambance cin bashin gwamnati da kuma cin bashin banki.

“Mu a nan (Najeriya) abinda ya tauye mu shi ne, shi malamin ba zai yi la’akari da wanda zai yiwa fatawa ba, shi ma mai tambayar sai dai ya tambayi malaman da ransa ya ke so, kamar misali da a ke magana a kan tattalin arziki, da yawa malamai idan

 ka yi magana kan irin kudin da gwamnatin tarayya ta ke bayarwa ta karkashin Babban Bankin Najeriya (CBN), don a je a karbi bashi, wanda za a gina masana’antu, a gina tattali arziki, malamai sai su rika fatawa a kai su na cewa haramun ne, saboda ‘interest’ (kudin ruwa), in ji shehin malamin.

Ya cigaba da cewa, “ka ga su wadannan malaman ba su gane bambamci tsakanin waccan magana ta gwamnatin tarayya da bankuna da za ka je ka ci bashi ba. Bankuna kamar irinsu Ja’iz Bank, First Bank, GTB, Union da sauransu mutum ya je ne cin bashi ne a matsayin kayan wani ya ba shi aro, amma wannan na gwamnatin tarayya hakkinka ne na dan kasa za a ba ka.

“Sai dai ba za a ba ka shi ba kai-tsaye, saboda Central Bank ba ya mu’amula da daidaikun mutane. Don haka ba za a ba ka kai-tsaye daga Central Bank ba, sai a ba ka ta bankuna. To, su wadannan bankuna ai ba za su zo su yi aikin banza ba. Don haka dole sai ka ba su wani abu, wanda shi ne kamar a ke ce da shi ‘administratibe charges’.

“To, sai ya zamana idan ma ka kira shi da suna ‘interest’ daidai ne, amma dai ya zamana cewa wannan hakkinka ne za ka je ka karbo, amma kuma ba za ka karbe shi ba, sai ka bayar da ‘interest’ (wato biyan hakkin wahalar da bankin su ka yi ma ka na shirya komai).”

Sheikh ya kara da cewa, “kamata ya yi su ’yan kasuwa da wayayyun mutane da duk wanda zai karbi kudi da su kansu malamai su gane cewa, wannan dukiya da gwamnatin tarayya ta ke cewa a je a ranta, ta na cewa a je a ranta ne a matsayin hakki ne na kowane dan Najeriya; dan Arewa ne, dan Kudu ne, Bahaushe ne, Bayerabe ne, Ibo ne, kowane irin jinsi ne kai a Najeriya hakkinka ne ka je ka karbi wannan abu, amma ga ka’idoji da za ka cika.

“Daya daga cikinsu ita ce ka biya bankin da zai yi ma ka aikin. Ko ka dauke shi a matsayin ‘interest’ ko ka dauke shi a matsayin ‘administratibe charge’ (kudin dawainiyar gudanarwa), duk wannan sai a ce ma ka babu laifi, ka je ka yi, saboda hakkinka za ka je ka karbo.

“Idan da misali kawai GT za ka je ka karbi bashi ko First Bank ko Zenith ko Union, to ka ga a nan ne za a zo a na maganar ko ya halasta ka karba ko bai halasta ba? Sai a dubi dalilin da ya halasta ko ya haramta, amma can kuwa (bashin gwamnati) ka je ka karba kawai.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!