Connect with us

KASUWANCI

CBN Ya Kafa Kwamitin Farfado Da Masaku 50 A Cikin Shekaru Hudu

Published

on

Sakamakon haramta shigo da  kayan aikin Masaku da akayi zuwa cikin Nijeriya daga kasar waje, don karfafa noman Auduga da sarafa kayan Masaku, a ranar Asabar data gabata, Babban Bankin Nijeriya CBN ya kafa kwamiti don farfado da noman Auduga da sarrafa kaya a Masaku.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele ne ya kafa kwamitin a babban birnin tarayyar Abuja, inda yace, ana sa ran

A cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele yace ana son a farfado da a kalla Masaku 50 nan da shekarar 2023.

Ya sanar da cewar, “Nijeriya har yanzu itace babba wajen samar da kasuwar Masaku, ya kara da cewar, muna son mu kubutar da fannin daga hannaun masu yin fasakaurin shigo da kayan aikin Masaku a cikin kasar nan.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele yaci gaba da cewar, zamu iya cin nasarar hakan ne ta hanyar gudunmawar hukumar hana fasakauri ta kasa da kuma sauran hukumomi dake kasar nan.

  Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele ya kara da cewar, kwamtin zai mayar da hanakali wajen farfado da noman Auduga da kara sarrafa ta da kuma samar da wutar lantarki ga Masakaun dake daukacin fadin kasar nan.

Acewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele, idan hakan ya auku, asarar da ake tabkawa ta sama da dala biliyan biyu saboda yin fasakauri a duk shekara don a daina yin wannan asarar.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele, CBN zai yi hadaka da hukumar yaki da fasakauri don kawo karashen yin fasakaurin kayan da ake yin amfani dasu a Masakun kasar nan.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele ya kara da cewar, za kuma ayi kokarin wajen rage tsadar gudanar da kasuwanci a cikin sauki a kasar nan, kawar da rubunya karbar haraji da kuma samar da ragi akan na’urorin da ake yin amfani dasu a Masakun.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele, ya sanar da cewar, tuni CBN ya janyo manoman Auduga guda  100,000  don noma kadadar Auduga 100,000 a cikin wannan shekarar ta 2019.

A karshe Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele yace a shirye yake don ya farfado da fannin don cimma burin da aka sanya a gaba.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da mataimakin gwamnan jihar Jigawa Barista Ibrahim Hassan da kuma mataimakin Kaduna Bala Barnabas duk sun halarci kafa kwamitin.

Nijeriya itace ta uku a nihyar Afirka wajen noma Auduga da fannin Masaku sai kuma kasar Masar da Afirka ta kudu take bi mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!