Connect with us

KASASHEN WAJE

Gangar Yaki: Trump Ya Ce Zai Rusa Iran Baki Daya

Published

on

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa muddin Iran ta kuskura ta kai hari kan muradun Amurka, Amurkan za ta rusa kasar Iran din baki daya. Gargadin na Trump ya zo ne kunshe cikin sakon da ya aike ta shafinsa na twitter, inda ya ce kaiwa muradin kasar hari zai ba da dama wargaza Iran baki daya, dan haka shugaban ya gargadi kasar da ta daina yi wa Amurka barazana.

Cacar baki a tsakanin kasashen biyu ta yi kamari ne bayan da Amurka ta tura jiragen ruwanta masu dauke da jiragen saman yaki yankin tekun Fasha. Sai dai wasu rahotannin sun nuna rarrabuwar kawuna tsakanin manyan jami’an gwamnatin Trump kan yakin, yayin da ake zargin mai baiwa Trump shawara kan harkokin tsaro John Bolton da tunzyra Amurka domin kaiwa kasar ta Iran hari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: