Connect with us

LABARAI

Gobe Buhari Zai Kai Ziyarar Aiki Jihar Imo 

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta kwana daya jihar Imo ranar Talata. Daga cikin abubuwan da shugaban jasar zai gudanar akwai bude kafaren filin jirgin sama na Sam Mbakwe International Cargo Airport.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan ya saka wa hannu,  Sam Onwuemeodo, ya bayyana cewa shugaban kasar zai bude sabuwar shelkwatar ‘yan sanda da babbar shelkwatar gidan yari.
A satin da ya gabata, mataimakin shugaban kasa  Farfesa Yemi Osinbajo shima ya ziyarci jihar don bude wasu muhimman ayyuka da gwamnan jihar Rochas Okorocha ya gabatar ciki har da wata kasuwar zamani mai suna Imo International Exhibition Centre.
Mataimakin shugaban kasa ya bude wadansu ayyuka da suka hada da gidan saukar baki mai suna Odenigbo Guess House,  da asibitin gidan gwamnati da da wasu titina da suka hada da Sam Mbakwe Road, Assumpta Road da Nnamdi Azikwe Road da ma wasu muhimman ayyukan, kafin zuwan shugaban kasar wasu sarakunan gargajiya a fadin kasar sun bude wasu ayyaukan a jihar lokacin da suka je taron zaman lafiya bayan an kammala zabe
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!