Connect with us

WASANNI

Kroos Ya Sabonta Kwantaragi A Real Madrid Zuwa 2023

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da cewa dan wasan ta na tsakiya, Toni Kroos  ya sake rattaba hannu a kwantaragin kungiyar zuwa karshe kakar wasan 2022/2023, a yau ranar Litinin.
Kafofin yada labaran kasar Spaniya suna ta rade raden cewa dan wasan tsakiyar kasar Germany mai shekaru 29  yana shirye shiryen barin kungiyar saodai dab wasan ya kara kwantaragin shekara hudu.
Ana sa ran cewa Real Madrid zata siyar da ‘yan wasan ta da dama sannan ta siyo wasu bayan tayi rashin kokari a kakar wasan bana, an siyo Kroos ne daga kungiyar Bayern Munich a shekara ta 2014 sannan ya buga wa Real Madrid wasa 233 tun zuwan sa kungiyar sannan ya lashe kofuna 11
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: