Connect with us

KASUWANCI

Badakalar Cin Hanci: Kasuwar Sayar Da Hannun Jari Ta Kori Jami’ai 33

Published

on

Kasuwar sayar da hannun jari ta kasa ta NSE ta soke jami’ai 33 saboda zargin cin hanci da rashawa. Hakan ya janyo basu chanchanci suyi dukkan wata hada-hada a kasuwar ba.

Jaridar Nation a cikin watan Disambar shekarar data gabata ta ruwaito cewar kasuwar ta sabunta dokokin ta don ta samu damar soke a wadanda take zargin da aikata cin hancin, inda Hukumar musayar kudi ta kasa SEC ta amince da sabuntawar a cikin watan Disambar shekarar data gabata.

Jerin manyan jami’an da aka soke a cikin sanarwar da aka samo a cikin satin da ya gabata ya nuna cewar, kimanin su 33 ne abin ya shafa da aka samu hannayen su dumu-dumu wajen aikata manyan laifukka da da ban-da- ban da suka hada da sayar da shiya ba bisa ka’ida ba, karkatar da kudi nuna rashin da’ar kwarewar gudanar da aiki, bayar da goyon baya don tabka aiyyukan almundahana a kasuwar.

Wadanda sunayen su ke ciki sun hada da, masu bayar da shawara akan sayar da shiya akawu-akawu, daraktoci, jami’ai, masu yin rijista, masu adana bayanai na fasaha, kwararu da sauransu.

A bisa fashin bakin da akayi akan wadanda abin ya shafa ya nuna cewar, masu bayar da shawarar siyar da shiya kusan rabin su an soke su, inda kuma sauran jami’ai, suma sunayensu na a kan gaba-gaba.

Har ila yau, duk wanda sunan sa ya shiga ciki, bazai kara amfana da dukkan wata dama ko alfarma ba, ko kara yarda dashi ba a kasuwar. Bugu da kari,

Irin wadannan da abin ya shafa, baza a kara basu wata damar yin hada-hada a kasuwar ba ko kara daukar su wani aiki a kasuwar ba.

Kamar yadda ka’idojinnsuka tanada, duk wanda aka soke a kasuwa, mai yuwa zai iya kara neman a sake mayar dashi kasuwar bayan ya kare wa’adin dakatar dashi da akayi ko kuma inda sokewar, ba anyi ta bane har abada ba ganin cewar kasuwar bata iyakance wa’adin ba.

Duk wani mutum da ya rubuta yana bukatar a cire sunansa daga cikin wadanda aka soke, don sake mayar da shi a kasuwar, dole ne ya bayar da cikakkun gamsassun bayanai da zasu goyi bayan dalilan sa na sake son dawo sa ko ita kasuwar.

Jaridar Nation a kwanan baya ta ruwaito cewar, anyi sokewar ce son a kara karfafa musayar kudia kasuwar, musamman yadda kasuwar take kokarin yin yaki da cin hanci da rashawa akan sayar da shiyar masu zuba jari a kasuwar ta hanyar badakala da karkatar da riba da wasu masu tafiyar da kasuwar suke yi.

A bisa binciken da aka gudanar a kasuwar ya nuna cewar, kimanin kashi 90 bisa dari na wadanda aka soke, an soke sune saboda sayar da shiyar abokan huddar su ba’a bisa ka’inda ba.

Sauran manyan laifukkan sun hada da, chanza alkaluman farashin shiya a kasuwar.

Har ila yau, jaridar ta Nation a kwanan baya ta ruwaito cewar, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC a yanzu hakan tana gudanar da bincike akan kimanin badakaloli 35 a kasuwar.

Sai dai cikakken bayanai akan shari’oin baza a iya bayyana su ba ganin cewar, har yanzu ana ci gaba da gudanar da shari’a akansu, amma bincike ya nuna cewar, mafi yawancin shari’un suna da nasaba da badakalar sayar da shiyar da kuma karkatar da kudin abokan hada-hada a kasuwar, da yin sojan gona da kuma tabka karyaryar gudanar da aiyyuka a kasuwar.

Kasuwar ta NSE ta hanyar kwamitin ta na ladabtarwa da kuma sashen tsaro na Hukumar musayar kudi ta kasa SEC ta hanyar kwatin ta na gudanar mulki suna kan gudanar da kwakwaran bincike don bankado dukkan badakalar da aka tabka a kasuwar dona kakaba takunkumi akan maau zuba jarin da aka samu hannun su a cikin badakalar.

Bugu da kari, NSE da kuma SEC basu da karfin ikon yanke wani hukunci, sai dai mahukunta a kasuwar sayar da hannun jarin, tuni suncike gibi akan nasu yin binciken da karfin iko da kuma rattaba hannun yarjejeniya ta (MoU) da Hukumar EFCC, inda hakan ya baiwa kasuwar ikon yin hadaka akan samar da bayanai, hukuntawa da kuma jaddada hukunci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!