Connect with us

KASUWANCI

Filin Jirgin Sama Na Benin Zai Fara Yin Aiki Da Daddare

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar, filin tashi da saukar jiragen sama dake garin Benin cikin jihar Edo a yanzu zai iya fara gudanar da aiki da dare da kuma lokacin da ake fuskantar haske kadan.

Hakan ya biyo bayan sanya na’urar haske dake taimakawa jiragen sauka a filin jirgin.

Karamin Ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika ne ya kadda ya kaddamar da na’urorin a satin da ya gabata a cikin daya daga cikin ayyukan da aka kammala a zangon farkon shugabancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Hadi Sirika yaci gaba da cewa, daga cikin ayyukan guda 157 da mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gada, inda kuma Gwamnatin Tarayya maici ta kirkiro ayyuka guda 130 ta kuma kammala su.

A cewar Karamin Ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika ana kuma shirin gina sabin wajen sauke kaya a filin jirgin na Benin, inda ya kara da cewa, a nan Benin, zamu gina sabn gurin sauke kaya a filin jirgin.

A cewarsa, “ Nan bada jimawa ba zamu fara gudanar da wasu aiyyukan kuma gwamnan jihar ta Edo ya yi alkawin bayar da dukkan hadinnkan da ya dace don a cimma nasara.”

Shi ma a nasa jawabin a lokacin kaddamar da na’urorin da aka gudanar a filin tashi da saukar jiragen saman dake Benin, Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki ya yo korafi akan gazawar da jiragen suke na sauka da dare da kuma lokacin da ake yin buji.

Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki ya kara da cewa, sakamakon kaddamar da na’urar ta ILS matsalar ta zamo.

A cewar Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki “ Daga yanzu kun samu na’urar hasken da zata ginga haskawa jiragen a lokacin tashi da kuma saukar su.”

Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki ya kara da cewa, na’urar zata ragewa direbobin jiragen saukin kasa ganin hanya a lokacin tashi da kuma saukar su da kuma magance matsalar buji.

Ya bayyana cewar, daga yanzu baza a dinga kule filin da karfe 6:00 na yamma ba, inda ya yi nuni da cewar, sakamakon samar da na’urar ayyukan filin jirgin zasu kara habaka.

A cewar Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki ya sanar da cewar, an gina filin na tashi da saukar jiragen na Benin ne sama da shekaru 60 da suka shige, inda ya kara da cewar, filin jirgin yana daya daga cikin tsofaffin jiragen sama da ake dasu a kasar nan.

Gwamnan jihar ta Edo Godwin Obaseki ya kuma nuna jin dadinsa akan daukaka matsayin filin jirgin, inda ya yi nuni da cewar, hakan zai kara habaka tattalin arzikin jihar harda kasa baki daya.

Gwamnan ya kuna sanar da cewar, Ma’aikatar Sufurin jiragen sama ta hanyar auna yanayi NiMET ta gina tare da bayar da kyautar tashar auna yanayi ga jami’ar Benin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!