Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rusa Da Gina Filin Jirgin Legas Kan Biliyan N14 – Sirika

Published

on

Gwamnatin Tarayayya ta sanar da cewar, ta ta kammala dukkan shirye-shuryen da suka dace don rusa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed dake cikin jihar, Legas.

GwamnatinbTarayyar ta ce tana shirin yin hakan ne Adin sake gina filin jirgin.

Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki a fannin na shekarar 2019 da aka gudanar a jihar Legas.

Acewar Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika, sake gina filin tashi da saukar jiragen na Murtala Muhammed ya zama wajibi, inda ya yi nuni da cewar, an gina filin jirgin na Murtala Muhammed ne yadda zai iya daukar fasinjoji guda 300,000 tun lokacin da aka gina shi.

Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika ya yaci gaba da cewa, amma a yanzu fasinjojin su dake yin tafiye-tagiye ta filin sun karu zuwa miliyan 8 a cikin shekaru uku da suka gabata.

Da yake yin tsokaci akan iya adadin kudin da aikin zai lashe Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika yace zasu kai naira biliyan 14 musamman don a yiwa filin zirgin gyaran da ya dace.

A cewar Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika, kafin a fara gudanar da aikin filin jirgin za’a mayar jiragen zuwa sabon gurin saukar jiragen da aka gina don su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Shi kuwa Manajin Daraktan Hukumar kula da sauka da tashin jiragen saman ta kasa FAAN shima ya sanar da cewar, za’a gusa da jiragen saman zuwa ga sabon gurinnda aka gina wanda har yanzu ake kan gufanar da sauran wasu ayyuka ake kuma sa ran kammala su kafin karshen wannan shekarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!