Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Tura Wa Jihohi Biliyan N691.560 Na Paris Club A Maris – Zainab

Published

on

Ministar kudi Uwargida Zainab Shamsuna Ahmed a ranar Litinin data wuce ta sanar da cewar, kudin baaussukan Paris Club naira biliyan 691.560 tuni aka rabawar da jihohin kasar nan a cikin watan Maris na shekarar 2019 bayan an tantance kudaden.
Uwargida Zainab Ahmed ta sanar da hakan ne a cikin sanarwar da Mai bata shawara ta musamman a fannin yada labarai da bayanai Mista Paul Ella Abechi, saboda labaran yamadidi dake yawo a wasu kafafen yada labarai cewar, nan bada jimawa ba za’a rabawar da jihohin kasar nan sauran kudaden da suka rage na basussukan Paris Club da ma’aikatar kudi ta tantance sun kai jimlar naira biliyan 691.560 saboda banbancin da aka samu a lokacin biyan, maimakon jimlar naira biliyan 649.434 da aka tantance.
Ministar kudi Uwargida Zainab Shamsuna Ahmed a cikin jawabin ta na kwanan baya a taron manema labarai na duniya data gudanar a babban birin tarayyar Abuja ta sanar da kamar haka, “Kudin karshe na basussukan Paris Club sun kai jimlar naira biliyan 649.434 Ma’aikatar kudi ta tantance su a matsayin sauran wadanda suka rage da za’a sake turawa jihohin dake kasar nan.”
Acewar Ministar kudi Uwargida Zainab Shamsuna Ahmed, “Biyan da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi a watan Maris na shekarar 2019, ya kai naira biliyan 691.560.”
Ministar kudi Uwargida Zainab Shamsuna Ahmed taci gaba da cewa, “Karin biyan da aka samu daga gun Babban Bankin Nijeriya CBN hakan ya auku ne saboda karinnda aka samu daga kudin muasa a lokacin biyan kudaden.”
A karshe Ministar kudi Uwargida Zainab Shamsuna Ahmed ta warware zare da abawa a kan cewar, babu wasu sauran kuadade na Paris Club da za a rabarwar da jihohin kasar nan, domin tuni aka rabar masu da kudaden a cikin watan Maris na shekarar 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!