Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Ta Samu Gibin Tiriliyan N15.69 A Kayan Cikin Gida A Shekaru Uku —NBS

Published

on

Nijeriya ta samu gibin naira tiriliyan 15.69 a kayan masana’antun cikin kasar da aka sarrafa a cikin shekaru uku, inda aka samu gibin jimlar naira tiriliyan 15.69 a kasuwancin da akayi a kayan da masana’antun cikinnkasar suka sarrafa a cikin shekaru uku da suka shige.
Wannan bayanain yana kunshe ne a cikin bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar, inda kuma hakan ya nuna cewar, Nijeeiya ta dogara ne kachokam akan shigo da kaya daga kasar waje don ta cimma bukatun da ake dasu na kayan a cikin kasar.
Daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2018, Nijeriya ta kashe naira tiriliyan 16.75 wajen shigo da kayan da aka sarrafa daga kasar waje, inda wannan shine mafi yawa da kudin ya kai naira tiriliyan 10.29 sama da kasafin kudi na naira tiriliyan 6.46 don gudanar da manyan ayyuka a cikin shekaru uku.
Nijeriya tayi kasafin naira tiriliyan 1.59 don kashe su akan manyan ayyuka a shekarar 2016, sai naira tiriliyan 2 a shekarar 2017 da kuma naira tiriliyan 2.87 a shekarar 2018 duk don gudanar da manayan ayyuka.
Har ila yau, Nijeriya ta kashe naira tiriliyan 4.65 akan kayan masana’antu data shigo dasu daga kasar waje a shekarar 2016, ta kuma kashe naira tiriliyan 4.65 a shekarar 2017 da kara kashe naira tiriliyan 7.46 a shekarar 2018, inda hakan ya kai jimlar naira tiriliyan 16.75 a cikin shekaru ukun da suka gabata.
A bisa sabanin hakan, Nijeriya. Ta samu ribar naira tiriliyan 1.06 daga kayan masana’antu data fitar waje a shekarar 2016 zuwa shekarar 2018, inda hakan ya nunabya kai kimanin kashi biyar bisa dari na jimlar kayan da Nijeriya ta shigo dasu cikin kasar duk a lokacin.
A shekara 2016, Nijeeiya ta samu ribar naira biliyan182.96 daga kayan masana’antu da aka sarrafa a cikin kasar aka kuma fitar dasu kasar waje, inda kuma yawan ya karu zuwa naira biliyan 232.06 a shekarar 2017 ya kuma kara karuwa zuwa naira biliyan 645.74 a shekarar 2018.
Dimbin sauran kaauwancin yana da yawa saboda surkushewar da wasu masana’antun Nijeriya sukayi, inda hakan ya sanya mafi yawancin yan Nijeriya suka digara kachokam akan kayan da kasar China take shigowa dasu cikin Nijeriya.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah ya sanar da cewar, Nijeriya tana yin iya kokarinta wajen ganin ta daina yin dogaro akan kayan da ake shigowa dasu cikin kasar, inda take kara yin kokarin fitar da kayan da masana’antun cikin kasar suma sarra zuwa kasar waje.
Akan masana’antun cikin gida kuwa, Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah yace, ma’aikatar sa ta mayar da hankali wajen wanzar da shirin farfado da masana’antun cikin kasar na NIRP.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah yaci gaba da cewa, kafa tsarin masana’antu na Nijeriya da kuma hukumar bayar da shawara akan masana’antu (NIPCAC) tana haifar da da mai ido a kasar nan.
Acewar Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah don a kara karfafa wanzar da shirin farfado da masana’antun cikin kasar na NIRP, anci gaba da gudanar da aiki akan shirin gangamin fitar da kayan da aka sarrfa a cikin Nijeriya na MINE, yadda za’a taimaka wajen kara ciyar da tattalin arzikkn Nijeiya gaba ta hanyar kara baiwa fannin masana’antun kasar nan goyon baya don kara ciyar da tattalin arzikin Nijeriya zuwa kashi 20 bisa dari nan da shekarar 2025.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah ya yi nuni da cewar, hakan kuma zai kara taimakawa wajen kirkiro da sababbin ayyukan yi kai tsaye miliyan 1.5 a masana’antun inda kuma a tashin farko za’a kara samun kari da kuma kara fadada ribar da ake samu ta dala biyan 30 ta kudin musayar kudin kasar waje nan da shekara 2025 a duk shekara ta hanyar kara fitar da kayan da masana’antun cikin kasar nan suka sarrafa.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah ya kara da cewa, sassan da aka samar na musamman na kasuwanci a cikin kasar nan, kamar na kashi na farko da aka fara garin Enyimba , dana sarrafa Aufuga a karamar hukumar Funtua cikin jihar Katsina dana yankin Lekki cikin jihar Legas, zasu taimaka wajen fitar da kayan da masana’antun cikin kasar nan suka sarrafa zuwa kasar waje.
Acewar Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah dibiyar ta taimaka matuka wajen bayar da manyan dauki wajen shawo kalubalen da fannin masana’antun kasar nan suke fuskanta, kamar maganar samar da isashiyar wutar lantarki da kuma samar da hanyoyi.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah ya buga misali da sahirin aikin hanya da habaka zuba jari da bayar da bashi na RIDRITCS wanda a karkashun shirin, masu masana’antun kansu suka mayar da hankali wajen daukar nauyin ginawa da gyara ayyukan hanyoyin dake daukacin fadin kasar nan.
Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah ya sanar da cewar, shirin matsakaita da kananan kasuwanci, zasu taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.
A karshe Ministan kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah yace, ma’aijatar sa ta samar da dimbin ci gaba, musamman wajen samar da damar samun kudi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!