Connect with us

TARIHI

Tarihin Nufe: Labarin Malam Dando

Published

on

Kashi Na Shida

Daga nan sai Malam Dando ya cigaba da zagaye ƙasar Nufe yana wa’azi da bayar da maganai. A haka ya ƙara samun kyautar wata mace baƙa kyakkyawa ta fuskar bada magani, ya mayar da ita ƙwarƙwarar sa. Itace ta haifa masa ɗa namiji Ibrahimu. Jimillar ’ya’yayen da a ka haifarwa Malam Dando cikin Nufe takwas ne, maza bakwai da mace ɗaya.
Bayan wannan, sai yaƙi ya auku tsakanin Sarki Majiya da Sarki Idrisu wanda a ke kira da suna Etsu Isa. Sarki Majiya ya fita zuwa Gbara ranar litinin cikin watan sha’aban, ya yi yaƙi sosai da Etsu Isa inda ya kora shi har zuwa Ilorin, a lokacin kuwa Malam Dando ya shiga tawagar Etsu Isa, don haka tare dashi akayi wannan gudun neman mafaka. Sa’annan Sarki Majiya ya koma garinsa Raba, su kuma suka cigaba da zaman su a Ilorin.
A na haka sai wata rana Sarki Majiya yake cewa da mutanen sa “ Ku sani ni sarki ne cikakke, ba ni da wani abokin faxa, gabas da yamma, kudu da arewa.”
Sai wani mabushin Bansanagi, watau Sarewa, ya ce ma sa “Ka da kace ba ka da wani abokin faxa da maƙiyi, ko ka mance da Sarki Isa da Malam Dando waxannan da su ke zaune a cikin Ilorin?”
Daga nan sai Sarki Majiya ya aika da takardu zuwa ga Sarkin Ilorin yace “Ina neman Sarki Isa da Malam Dando, ina so ka aiko mini da su.”
Shi kuma Sarkin Ilorin sai ya rubuta takardar sulhu zuwa ga Sarki Majiya, amma sai Sarki Majiya yaƙi Sulhu. Ya sake rubuta takarda cewar “Na baiwa Mutanen Ilorin duka gaba”.
Sai kuwa Sarkin Ilorin yace “Allah shine muke neman taimako duka a wurinsa, ya taimake mu in yaso.”
Sarki Majiya ya fidda yaƙi ranar Jumua cikin watan shawwal, ya sauka a bakin wani rafi da ake kira da suna Ansa. Da saukar sa sai mayaƙan Ilorin suka riske shi, suka auka masa da yaƙi.
Da fari sarkin ya soma cin galabar su inda har ya shiga cikin garin Ilorin, amma sai suka ƙara ƙaimi inda suka kore shi kora mai tsanani, ya koma wajen gari.
Sarkin Ilorin ya tara malaman Ilorin duka yace ko akwai wani malami wanda zai taimakeni akan wannan abokin gaban?” Duka suka ce “Ba mu da wani taimako wanda zamu taimake ka da shi.”
Sai Malam Dando yace masa “Ni fa ina da taimakon da zan bayar, domin na fuskanci malamai da kuɗi zambar ɗari uku da dubu bakwai na sami asiri”
Sarkin Ilorin ya ce “To kuwa Zan ba ka zambar dubu saba’in”. Malam Dando yace “Ijarata da kai abin da aka samu a cikin damfamin Sarki Majiya.” Sarkin Ilorin ya ce “ Na ƙara maka da damfamin Sarki Majiya na biyu idan da akwai”.
Sa’annan Malam Dando yace a nemo masa mazaje uku, ya fita wajen gari dasu da shirin yaxi, suka sauka nesa da sansanin Sarki Majiya, sannan yace da mazajen su haƙa masa rami mai zurfi dai dai da tsawon mutum, sannan yayi bukkah ya xibiya ta akan ramin ya shiga cikin ramin kwana uku, sannan ya fita zuwa Ilorin da hantsi.
Da shigar sa ya riski Sarkin Ilorin yace masa “Ina sarkin Yaxin Ilorin?” Sarki yace Aliyu shine Sarkin yaxi. Sai Malam Dando yace a nemo masa hankaka, sarkin yaxi ya biyo ni da tawagar sa da hanzari”
Ai kuwa nan take akayi kamar yadda yace. Malam Dando ya aikata asiri a bakin hankakan, ya baiwa Aliyu Sarkin yaxi shi yace masa “ kada ka saki hankakan nan har sai ka kusanci sarki Majiya”
Sarkin yaƙi Aliyu ya fita ta kan ganuwa kusan faɗuwar rana, ya zagaya ta yamma yabi wuraren da Sarki Majiya yayi sansani sannan ya saki hankakan nan, ya tashi fir zuwa laimar sarki Majiya, ya yi ƙara, nan take hankulan kowa na tawagar ya tashi, suka ruɗe, dukkan su suka bazama a guje yaƙin su ya karye, mutanen Ilorin suka samu riba dasu.
Su ka kama dawaki zambar ishirin da huɗu, da mataye ɗari takwas dake cikin damfamin Sarki Majiya.
Sai Malam Danbo da Etsu Isa suka fita daga cikin Ilori suka koma Raba da zama bayan korar Sarki Majiya. Malam Dando ya ce wa Sarki Isa “zauna a wannan gari” Sarki Isa yace ni bani zama cikin garin abokan gaban mu. Ni ina nufin zama a wani wuri ne da ake ce masa Jangi” Watau ya yiwa Malam Dando Musu.
Daga nan Malam Dando ya zama mai iko da Juguma, ƴaƴansa ke karɓo harajin sauran ƙasashe duka, har daga baya kuma saɓani ya ƙara aukuwa tsakanin sa da Etsu Isa wanda yayi silar aukuwar yaƙi gagarumi a tsakanin su.

Kashi Na Bakwai

Tun bayan wancan yaƙi, sai Sarki Majiya ya koma Juguma da zama, anan ya cigaba da mulki har ya rasu.
Akwai watarana da Malam Dando ya aika masa da cewa “Ka komo garinka Raba da ka tashi”. Sai Sarki Majiya ya mayar masa da cewa “Mu Nufawa ɗabi’armu ba mu komawa garin da yaxi ya ci sai an qone shi, don haka zan zauna a Juguma”.
Amma dalilin yaƙi tsakanin Malam Dando da Etsu Isa akan kuɗin haraji ne wanda ƴaƴan Malam Dando suka rinka zagayawa suna karɓa.
Etsu Isa yace “Ashe Malam Dando yana son mulkin duniya ne tun da har yake aika ƴaƴansa cikin ƙasashe domin su karɓi haraji? Yana neman duniya domin kan sa ne ba domin mu ba, shine har muka biye masa muka kori ƴan uwanmu suka gudu wani wuri shikuma ya karɓe sarautar su?”
Don haka sai ya aike masa da cewa “Ni bana son ƴaƴanka su ƙara karɓar haraji a ƙauyen mu bayan wannan shekarar”.
Malam Dando ya aiki manzon sa ga Sarki Majiya a lokacin da ya koma ƙasar Basa da zama da cewa “ Ka dawo ƙasar ka da zama, ka sani yanzu babu amana tsakanina da Etsu Isa, bayan na taimakeshi yanzu ya zama abokin gaba ta”.
A lokacin ne Sarki Majiya ya koma Juguma da zama saboda al’adar su ta Nufawa da ta sanya ba zai iya komawa Raba ba. Har mutuwa ta riske shi kuwa yana Juguma inda aka naɗa ɗansa Chado ya gaji shugabancin sa.
Shi kuwa Etsu Isa sai ya shirya yaƙi zuwa Raba don tumɓuke Malam Dando a mulki.
Malam Dando ya shiga Halwa ta kwana uku da yaji labarin zuwan sa. Ya fita halwa aƙarshen rana ta uku ya bi turba , ƴaƴansa suka fitad da sansani suna biye dashi riƙe da makamai har zuwa bakin kogi.
A wannan rana yaƙi yazo har bakin kogin nan ta wani waje da ake kira Jabara, a ranar ne ɗan Malam Dando Ibrahim ya rasu a idon ubansa, a lokacin da ake tsaka da gwabza yaƙi. Da yaƙi yayi tsamari kuwa sai Etsu Isa ya gudu da tawagarsa ya koma Kaniya da zama. Bai ƙara ɗagawa Malam Dando kai ba har mutuwa ta riske shi yana sarkin Kaniya, inda aka naɗa ɗansa Mu’azu magajinsa.
Shi ma Malam Dando ya cigaba da zama a Raba har mutuwarsa, inda ɗansa Muhammad Saba ya gajeshi tare da ɗorar da yaƙi ga sauran ƙasashen Nufe, har takai ya samu iko sama da kusan ɗaukacin sarakunan dake ƙasar Nufe kafin daga bisani faɗace faɗace su raunana shi tsakanin sa da ƴaƴayen sarakunan nan da ubansa ya gwabza dasu watau Majiya da Etsu Isa da kuma tsakanin sa da ƴanuwansa ƴaƴan Malam Dando masu biɗar sarauta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: