Connect with us

FILIN FATAWA

Na Auri Amare Biyu A Rana Daya, Me Yakamata Na Yi Wajen Tarewa?

Published

on

Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya auri mata biyu (sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga? Nagode Allah Ya karawa malam imani.
Amsa:
To dan’uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auran mata biyu a yini daya, saboda hakan zai kawo matsala wajan bawa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara da ita, to dayar za ta cutu, saidai idan hakan ta faru, to zai fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, in kuma sun shigo tare ne sai ya yi musu kuria. Don neman karin bayani duba : Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na : 981. Allah ne ma fi sani 5

Manufofin Da Suka Sa Aka Haramta Zina!
Tambaya:
Assalamu alaikum malam, Ina son karin bayani game da manufofin sharia akan haramta zina.
Amsa:
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya zo don ya kare tsatson Dan’adam da mutuncinsa, don haka ya shar’anta aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin da haramta zina ya kunsa : 1. Katange mutane daga keta alfarmar shari’a. 2. Samar da Dan’adam ta hanya mai kyau, ta yadda za’a samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi ta hanyar zina, to ba za’a samu wanda zai kula da shi ba yadda ya kamata. 3. Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna. 4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja. 5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a bayyane. 6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa, sai fitintinu, su yawaita. 7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane. 8. Kare mutuncin yaron da za’a Haifa, domin duk yaron da aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Wanda Ya Auri Mace Saboda Kyanta?
Tambaya:
Malam : Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin kyan, ko dan kudinta kawai Allah zai hana masa jin dadin kudin, shin kuwa hadisin akwai shi kuma ya inganta?
Amsa:
Ga yadda aka fadI hadisin : duk wanda ya auri mace saboda kudinta, Allah zai kara masa talauci, duk wanda ya auri mace saboda kyawunta Allah zai kara masa muni, saidai a cikin maruwaitan hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba, kuma ba za’a kafa hujja da shi ba. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Auren Kirista
Tambaya:
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa?
Amsa :
To dan’uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu da Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma’ida aya mai lamba ta : (5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan – halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah Ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794 Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu . Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka’idojin musulunci.

Shin Baiko Aure Ne ?
Tambaya:
Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min kauli-da-ba’adi, akan cewa, ai mun riga mun yi aure, ni dai gaskiya malam na ki yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?
Amsa:
To ‘yar’uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne saboda hujjoji kamar haka: 1. Abin da aka sani shi ne kudin da ake bayarwa yayin baiko ba’a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunkulewa su bayar gaba daya, kin ga kuwa in haka ne, to ai dukkan aiyuka ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito. 2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa da kudinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne. 3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan wani ashararu zai iya kai kudi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna. 4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kudin da za’a yi baiko, zai iya zama mutum daya, kin ga akwai nakasu kenan. 5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban. 8 6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado tsakanin wadanda aka yiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin ma’aurata suna gadon junansu . Allah ne ma fi sani .

Hukunci Saduwa Da Mai Ciki
Tambaya:
Malam na kanji wasu mutane na fadar cewa 8at a halatta idan matar mutum tana da juna biyuyayi jima’I da ita har sai ta haihu, meye gaskiyar maganar?
Amsa:
To dan’uwa ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” Abu-dawud : 1847 Ibnul kayim yana cewa :”Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka 8at a ruwa” Tahzibussunan 1\193 . Masana likitanci suna cewa: Ba’a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron . Sannan yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan. Allah ne ma fi sani.

Mijina Ba Ya Sallah, Ko Zan Iya Neman Ya Sake Ni?
Tambaya:
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka .
Amsa:
To ‘yar’uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta : 81. Ga shi kuma aya : 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce. Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta : 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta : 616 ya tabbatar da hakan, Saidai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku. Allah ne mafi sani. Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: