Connect with us

SIYASA

Abin Takaici Ne Yadda Gwamnatin Buhari Ta Gaza Showa Kan Matsalar Tsaro- Jigo A APC

Published

on

Tsohon dantakarar Majalisar Dokoki ta jihar Kaduna a karkashin inuwar jamiyyar sa ta APC mai mulki Alhaji Abdullahi Gambo Abba ya sanar da cewar, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin alummar da Allah ya dora mata nauyin yi.
A hirar sa da manema labarai a garin Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba wanda numa shine Jakadan Hayin Banki a garin na Kaduna, yace, gwamnatin Shugaba Buhari ta jefa yan Najeriya, musamman wadanda sukea yankin Arewacin kasar nan a cikin muwu yacin hali na rashin kare rayukan su da kuma dukiyoyin su.
Jigon a jamiyyar APC Alhaji Abdullahi Gambo Abba yaci gaba da cewa, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kargar mulkin kasar ya saita an, lamarin tsaro, musamman wajen yaki da yan ta’adda da suka addabi alummar Arewa maso gabas, amma daga baya sai gwambatin ta yi sako-sako, inda ya danganta hakan raunin shugabanni tsara rundunar soja dana ‘yan sanda, hakan ya kuma kara baiwa kungiyoyin ‘yan ta’adda kara mike kafa don aikata ta’addancin su, musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Alhaji Abdullahi Gambo Abba ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta sauye-sauyen manyan jami’an tsaro, musamman ta hanyar sanya masu jini a jika don kawo karshen matsalar rashinntsaro a kasar nan, musammanna Arewacin kasar.
Jakadan na Hayin Banki ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yiwa Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abudulmumin Kabir Usman ta’aziyar manoma sha takwas da yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Batsari.
A karshe Abdullahi Abba ya roki daukacin alummar kasar dasu dukufa wajen gudanar da addu’o’i domin samun sauki akan matsalar tsaro da ke addabar kasar nan, musamman a wasu jihohi dake Arewacin Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: