Connect with us

SIYASA

An samu Tashin Farashin kayan masarufi Da Kashi 11.37 A Afirilun 2019 –NBS

Published

on

Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta sanar da cewar, jaddawalin farashi na CPI da ake yin awon hauhawan farasahi, ya nuna cewar hauhawan farashi ya kar zuwa kashi 11.37 bisa dari a cikin Afirilun 2019.
Bayanin na NBS yana kunshe ne a a cikin rahoton ta na ma’aunin CPI hauhawan farashin na Afirilu, data fitar a ranar Larabar data gabata a garin Abuja.
Acear Hukumar, wannan ya kai kashi 0.12 sama da yawan wanda aka samu a Maris din 2019 wanda ya kai kashi 11.25 bisa dari.
NBS ta kara da cewar, sai dai, hauhawan farashin ya karu ne saboda tashin farashin wasu kayan masarafun.
Rahoton ya yaci gaba da cewa, jaddawalin farashin na kayan masarafi ya nuna cewar, ya kai kashi 13.70 bisa dari a Afirilu idan aka kwatanta da kashi 13.45 bisa dari a Maris din 2019.
Acewar rahoton, jaddawalin karin alan kayan masarufin ya nuna cewar, tashin farashin ya shafi Nama, Kifi, Manja da Mankuli, Burodi, Madara, Kwai, Doya , kayan marmari da sauransu.
Daga wata zuwa wata, rahoton ya yi nuni da cewar, jaddawalin kayan masarafi ya nuna cewar, farashin ya karu zuwa kashi 1.14 a Afirilu daga kashi 0.26, inda kuma a Maris aka samu kashi 0.88.
Rahoton ya sanar da cewar, ana shekara daya, jaddawalin musayar kayan masarufin wanda ya kare a karshen Afirilu, ya kai kashi 13.34, inda rahoton ya kara da cewa, wannan ya kai kashi 0.08 daga yawan wanda aka samu kashi 13.42 a Maris.
Sai dai, rahoton na NBS ya yi nuni da cewar, karin ya danganta ne akan irin nau’ukan abincin da mutane suke ci ne.
Hukumar ta kara da cewar, a wata-wata- jaddawalin karin ya kai kashi 0.94 a Afirilu, inda hakan ya nuna cewar, ya kai kasa da kashi 0.15 da kuma kashi (0.79) a Maris.
NBS ta sanar da cewar, jaddawalin na CPI a cikin watanni sha biyu da ya kare a karshen Afirilu ya nuna cewar, ya kai kashi 11.3.
A cewar rahoton na NBS, adadin ya nuna cewar ya kai 0.09 daga kashi 11.40 da aka samu a Maris.
Rahoton na Hukumar NBS ya yi nuni da cewar, hauhawan farashin da aka samu a cikin birane ya karu da kashi 11.70 a cikin Afirilu daga kashi 11.54 da aka samu a Maris.
A karkara kuwa rahoton yace, hauhawan farashin ya karu da kashi 11.08 a Afirilu daga kashi 10.99 a Maris na shekarar 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: