Connect with us

MANYAN LABARAI

Dan Takarar PDP Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Zamfara -INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a yau Asabar, ta amince da hukuncin da kotun koli ta yanke a kan babban zabe na kasa na jihar Zamfara inda kotun ta sanar da cewa ‘yan takarar jam’iyyar PDP ne suka lashe zaben jihar.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da manema labarai a garin Abuja cewa zamu ba zababben gwamna da mataimakin sa tare da ‘yan majalisar dokoki uku da na wakilai bakwai takardar shaidar lashe zabe ranar Litinin da karfe 2:00 na rana.

Idan ba’a manta ba a jiya ne kotun koli ta bayyana cewa ta soke dukkan kuri’un da jam’iyyar APC ta samu a zaben da aka gudanar a jihar Zamfara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: