Connect with us

LABARAI

Mako Guda Ya Mika Mulki: Gaidam Ya Amince Da Ware Biliyan 6.1 Don Karasa Filin Jirgi

Published

on

Mako guda ya mika ragamar mulkin jihar ga zababben gwamna;ai Mala Buni, 29 ga watan Mayu, 2019- Gwamnan Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya amince da ware naira biliyan shida da digo daya da yan kai (N6.1b), a zaman majalisar zartaswa, a ranar laraba.
Bayanin cimma wannan matsayar ya fito ne daga kwamishinan yada labarai da al’adu a jihar Yobe, Mala Musti jim kadan da kammala zaman majalisar zartaswar jihar.
Alhaji Mala Musti ya ce, zaman ya amince da ware naira biliyan biliyan 6,067,305,786.91 domin bunkasa taswirar kammala ginin filin jirgin sama na kasa da kasa da jihar Yobe ke ginawa, a Damaturu.
Bugu da kari kuma, gwamnatin ta ware naira miliyan 127 domin gudanar da ayyukan aikin hajjin bana, 2019.
A hannu guda kuma, wannan lamari ya jawo takaddama kala-kala tare da tofa albarkacin jama’ar jihar Yobe, yayin da wasu ke ganin rashin dacewar hakan, a daidai irin wannan lokaci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!