Connect with us

MANYAN LABARAI

Rigakafin Ambaliyar Ruwa: Jihar Kano Za Ta Kashe Miliyan 119

Published

on

A yau Asabar ne gwamnatin jihar Kano ta ce ta shirya kashe kimanin Naira miliyan 119 don yashe magudanun ruwa a garin Kano don gujewa ambaliya.  Kwamishinan kula da muhalli, Dakta Ali Makoda, ya sanar da hakan a yau Asabar bayan lura da aikin tsaftar muhalli a Kano.
Makoda ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta na kokarin tabbatar da tsafta da lafiyar muhalli.
‘Wannan ya sa ya zama wajibi mu yashe magudanan ruwa a kowace shekara,” inji shi.  Ya ce banda kokarin gwamnati, akwai bukatar mutane suyi aiki tare don tabbatar da tsaftar muhallin su.
Makoda, wanda ya ce wannan shi ne karo na karshe da zai iya lura da aikin tsaftar muhallin wata wata a matsayin Kwamishinan muhalli ba, ya nuna farin ciki da gudunmawar da jama’a suke bayar wa wajen tsaftar muhalli, Makoda ya bukaci kwamishinan da zai maye gurbin sa a matsayin Kwamishinan lura da muhalli ya ninka kokarinsa domin a ci gaba da samun tsaftaceccen muhalli
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!