Connect with us

LABARAI

Sunayen ‘Yan Takarar PDP 36 Na Zamfara

Published

on

Kafin hukuncin da kotun koli ta Nijeriya ta fitar jiya Juma’a, dukkan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zabukan da suka gabata, sunansu wadanda suka fadi a zabe. Kotun koli ta bayyana sunayen mutum 36 dukkansu ‘yan jam’iyyar PDP ta adawa a matsayin wadanda suka lashe zabukan guraben mukamai daban-daban.

Guraben sun hada daga na gwamna da mataimakin shi, da na sanatoci uku, ‘yan majalisar tarayya bakwai, sai ‘yan majalisar jiha su 23. Kotun ta damka dukkan kujerun ga jam’iyyar PDP wacce ita ce ta zo ta biyu a zabukan da aka gudanar a jihar Zamfara din, bayan da kotun ta yake cewa jam’iyyar APC ba ta da hallaccin tsayawa a zaben.

Bello Matawalle ne wanda ya lashe Gwamna, sai Mahdi Gusau a matsayin mataimakin Gwamna. Ya’u Sahabi ne Sanata mai wakiltar Zamfara ta arewa, sai Mohammed Hassan, Zamfara ta kudu, Lawani Hassan, Zamfara ta yamma.

Kujerun ‘yan majalisar tarayya bakwai sune; Umar Dan-Galadima –mazabar Kaura-Namoda/Birnin Magaji,
Bello Hassan Shinkafi –mazabar Shinkafi/Zurmi, Kabiru Amadu –mazabar Gusau/Tsafe, Shehu Ahmed –mazabar Bungudu/Maru, Kabiru Yahaya – mazabar Anka/Talata Mafara, Ahmed Bakura – mazabar Bakura/Maradun, Sulaiman Gum– mazabar Gummi/Bukkuyum.

‘Yan majalisar jiha sune:

Zaharadeen M. Sada – Kaura Namoda ta arewa, Nura Daihiru – Birnin Magaji,
Salihu Zurmi – Zurmi ta gabas,
Nasiru Muazu– Zurmi ta yamma,
Muhammad G. Ahmad – Shinkafi,
Musa Bawa Musa – Tsafe ta gabas, Aliyu Namaigora – Tsafe ta yamma, Ibrahim Naidda – Gusau ta gabas,
Shafiu Dama – Gusau ta yamma,
Kabiru Magaji – Bungudu ta gabas,
Nasiru Bello Lawal – Bungudu ta yamma, Yusuf Alhassan Muh – Maru ta arewa, Yusuf Muhammad – Anka,
Shamudeen Hassan – Talata-Mafara ta arewa, Aminu Yusuf Jangebe – Talata Mafara ta kudu, Tukur Jekada – Bakura,
Faruk Musa Dosara – Maradun I,
Nasiru Atiku – Maradun II, Abdulnasir Ibrahim – Gummi,
Mansur Mohammed – Gummi II, Ibrahim Mohammed Naidda – Bukkuyum ta arewa, Sani Dahiru – Bukkuyum ta kudu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!