Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Bindiga 43 A Bauchi

Published

on

Hukumar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa ta samu nasarar kame mutane 43 da ake zargi da aikata manyan laifuka wanda ya hada da fashi da makami da yin garkuwa da mutane, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu Sani, ya bayyana hakan a cikin jawabinsa da ya gabatar a yau Asabar a lokacin gabatar da sabon atisaye mai suna: ‘Sectoral Community Policing’ don inganta tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa daga cikin mutane 43 da aka kama ana zargi,  an yanke wa takwas daga ciki hukunci, yayin da 35 ke jiran shari’a.

Sani ya ce; Yana da mahimmanci a wannan lokacin ku sani  cewa, tare da wannan tsari, an bincike da yawan laifukan da ake aikatawa  a jihar.  An kama mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka daban daban da suka hada da: Sara-Suka , Babeli,  mallaka jabun dala, amfani da miyagun kwayoyi.

‘An yanke wa  mutum takwas da ake tuhuma daga ciki hukunci yayin da 35  ke hannun ‘yan sanda suna gudanar da bincike.’ inji shi
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: