Connect with us

MANYAN LABARAI

Sarkin Katsina Ya Ce Bana Ba Za A Yi Hawan Sallah Ba

Published

on

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumin Kabir Usman ya sanar da cewa an soke hawan sallah wannan karon don nuna jimamun su ga abubuwan dake faruwa ga al’ummar jihar. Har ila yau, masarautar ta mika sakon ta’aziyya ga dukkanin al’ummar jihar akan ibtila’in da ya faru na kashe mutanen garin Batsari, Dan Musa, Kankara da Wagini da sauran garuruwa da lamarin ya shafa.

Sakataren masarautar garin Katsinan Alhaji Bello, ne ya fitar da sanarwar, inda ya shaida wa al’umma cewa sakamakon yanayin da al’ummar jihar suka tsinci kansu na jimami da alhini, masarautar ta yanke shawarar ba zata gabatar da hawan sallah ba a wannan karon

Alhaji Bello ya bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumin Kabir Usman CFR, da ‘yan majalisarsa suka ga ya dace a soke duk wasu harkokin shagulan biki domin su nuna jimamin su kan abinda ya faru ga al’ummar jihar.

A karshe sanarwar ta bayyana cewa za aje ayi sallar idi kamar yadda aka saba, sannan za ayi addu’o’i na neman zaman lafiya ga jihar ta Katsina da ma kasa baki daya
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: