Connect with us

ADABI

Zuwan Malam Bahaushe Afrika Ta Yamma, Rayuwarsa Da Sana’o’insa (3)

Published

on

Ci gaba daga makon jiya

Sabanin yanda mu ka furta a baya kyas, a wata ruwayar an nuna cewa Mallam Bahaushe a Kasar Hausa ya soma ne daga wani yanki ko wasu yankuna na Kasar Tahoua ta Kasar Nijar da ake kira Illela (ko Lalle da Boso) An ce daga nan Hausawa su ka fallatsa zuwa sauran sassan Arewaci da kudancin Afirka. Farfesa Ado Muhamman, shugaban Jami’ar Tahoua, a wata zantawa da mu ka yi da shi ya nuna cewa tun usulan akwai Hausawa na gidi (na asali) da su ke zaune a nan yankunan kasar Tahoua da a da ba su taba zuwa ko’ina ba sai daga baya su ka fantsama cikin Duniya su ka yi sansani. Irin Hausar su ma ta zo daidai da irin Hausar Kasar Sakkwato da Kwanni. Watau tatattar Hausa ce ba ta da gami ko surki. Daga cikin su akwai ma masu tsaga irin ta Bahaushe na asali. Bugu da kari har yanzu ba su daina yin irin waccan al’ada ta Malam Bahaushe na farko ba, duk da yak e addinin Islama ya zo ya kawo sauye-sauye da gyare-gyare ga al’adojin da ya tarar.


Nan da nan fa gadan-gadan sai Malam Bahaushe ya himmatu wajen aiwatar da sana’o’i. Wannan hanyoyi ne na inganta tattalin arzikinsa da na iyalinsa. Daga cikin su akwai wadanda ya gada tun daga kan kakanninsa. Kamar su noma da kiwo da kuma uwa uba fatauci. Sun taimaka ma Hausawa wajen kawo zaman lafiya da zumunci ma a tsakanin su. Domin a wancan lokacin, kowanne mutum bahaushe ya dauki irin sana’ar da ya gada a gidan su da matukar muhimmanci. Ina? Ba ka is aka tsallake gidan ku ka tafi wani gida ka yi ko ka koyi irin sana’ar sub a, kai ga na ka? To ita sana’ar gidan ku w aka bar ma wa ya yi? Ka ga ba ta yiwuwa. A wancan wakati kuma bahaushe bai isa ya tsallake maganar iyayen sa ko magabatan sa ba. Wurin Malam Bahaushe aka ga wannan halayyar.
Makasudin kowa ya rike sana’ar gidan su shi ne don kada gidan yam utu, sannan kuma kowa ya dogara da kan sa don a lokacin ba a san maula ko zuwa wurin wani don nuna halin kaskanci ba. Wannan shi ya kara daga martabar Mallam Bahaushe ya nuna shi a idon Duniya a matsayin wani muhimmin mutum, karimi. Kuma sannan da yaro ya fara girma sai a nuna masa sana’a irin ta gidan su.


Misali, noma shi ne sana’ar Malam Bahaushe na farko. Noma shi ne ma kashin bayan tattalin arzikin kasa. Noma sana’a ce ta kowa da kowa, kama daga mai arziki zuwa talakka, ko mace ko namiji, ko babba ko yaro. Lokacin da wani Bature jar fata Ba’ingile da ake kira Dokta Henrich Bath dan yawon Duniya ya zo Katsina cikin shekarar 1850 daidai ya hudo ma garin ta arewa, watau daga kasar Tasawa. Ya bayyana cewa da ya ratso ya ga babu saura ko fili wanda ba komi a cikin sa. Ko’ina gonaki ne na jama’a. Ya kuma ga jama’a sun noma dawa da gero da taba da auduga da dankali da makani da sauran su. Wannan ya samu nasara ne domin Kasar Hausa kaf din ta ta na da fadamu na noma da jigawa masu albarka gami da yawan ruwan sama matsakaici.
Hausawa sun fara yin tunanin zama wuri guda don su rika yin ayyuka tare, su taimaki kawunan su su kuma yi aikin gayya tare.
Babban misalin da za mu buga a nan shi ne kewayen Birnin Katsina tun gabanin zamanin mulkin Sarki Muhammadu Korau (1388-1448) A cikin littafin sa, R. Soper ya tabbatas cewa kushewoyin da aka samu a wuraren da ke kusa da birnin Katsina ya nuna cewa akwai jama’a a wuraren tun shekaru aru aru da su ka gabata Wadannan Adawa su na da girma sosai kuma ba su da wata sana’ar da ta wuce kere-kere na kayan halbi, su kan shiga jeji su kashe manyan namun jeji. A cikin karni na 15 kewayen birnin Katsina ya cika da jama’a da fatake masu tasowa daga kudu su nufi arewacin Katsinar. Dalilin bunkasar Katsina kenan, wadanda su ka fara kafata su ka shiga kafa kan makeru a inda su ka sami matsugunni suna yin kira. Wannan wata dabara ce da su ka bullo da ita ta maishe da karfe abin amfani ga dan Adam. Sannan a hankali mutanen su ka fara kera makaman yaki da na noma, kamar; bindiga, fartanya, gatari, dagi ko diga, sarka (ta doki), wuka, adda da dai sauran su, su na fansar wa fatake ma su zuwa su yada zango su wuce kasashen Nijar kamar Maradi, Damagaran, ko Yamai, da sauran ayarin manoma. Mutum guda, a bisa kan makerar sa sai ya yi hauya sama da dari ukku (300) Wannan shi ya sanya suma mahalba da manoma su ka kulla kawance da makera, har su ma su ka zo su ka kafa sansanin su. Har ya zuwa wannan wakati na karni na 15 babu wuri ko kudi na ciniki a wannan zamani sai dai abin da su ka kira ‘ba-ni-in-baka’, wanda Turawa ke ce ma trading by bata. Ma’anar haka shi ne su manoman sai su ba makeran gero da dawa ko masara, da sauransu. Su kuma makeran sai su mayar masu da abubuwan da su ka kera. Mahalba kuma sai su ba makeran dan naman dabbobin da su ka halbo ko wasu abubuwan daban, su kuma su basu kayan halbin da su ka kera.
Ko wannensu a cikin ukkun ya dogara akan kowanne kan zaman sana’ar sa. A daidai lokacin kuma wannan wuri ya kara bunkasa, domin ana ma tunanin unguwar Ambuttai aka fara kafawa a cikin birnin Katsina, to daga nan sai kananan sansani na kewaye da ita su ka tsira. Mahalba na sare itacen su na mayar da su itacen bindigogi. Makera kuma, wadanda a sa’annan a ka fi kira da ‘yan tama su na saro itace su na konawa, su na kuma amfani da garwashin wajen gasa karafa. Cinikin tama fa ya gawurta.
Wannan bauta a na yin ta a ko’ina a cikin Arewacin kasar nan. Kamar dai yanda mafi yawancin jama’a ke yi, na zamani na baya, mutanen Katsina sun samu matsalar fahimtar wanene Ubangiji. Kuma su ka rasa gane shin minene bambanci a tsakanin Ubangiji da rana da wata da taurari da ma sararin samaniya da haske ko walkiya ta lokacin ruwan sama da kuma tsawa. Kowanne sun dauka shi ne Allah. Saboda jahilcin ma hatta duwatsu an sha bauta masu, ana cewa daga sama su ka fado, wai daga duniyar Marik.


Amma shima Sheikh Abu Abdallah Muhammad bin Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil ya san cewa wasu abubuwa da su ka shafi addinin musulunci da ya ke so Sarkin Katsina da jama’arsa su jaddada ba su yiwuwa. Akwai abubuwa da dama da su ka shafi al’adu da siyasar wannan lokaci da shima ya san ba su baruwa a Katsina da Kano kamar yanda ya je Katsina ya tarar. A cikin littafin Tarikh Asli Katsina wa Asli Ghubir an bayyana cewa shi wannan bawan Allah shi ya ma kai addinin musulunci Katsinar. Abinda kuma ya sanya cikin lokaci kankane aka yarda da abin da ya kawo shine da bai sa abinda ya shafi son zuciya ko abin Duniya ba, ya zo da abin da Alkur’ani maitsarki ya kawo ne. Tuni wasu masu sha’anin mulki a kasar Katsina su ka amshi kiran Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil su ka kuma fara aiwatar da mulki kamar yanda ya zo daga koyarwar Annabi Muhammad (SAW) Shi kuma Sarkin Katsina Ali Murabus sai ya maishe da gidan Korau kamar wani wurin yin taro ko ganawa a yanda za a kare garin daga mahara. A takaice ya ma kirkiro rundunar sojoji ko dakarun yaki da su ka shata iyaka tsakanin Katsinar da Kano, a lokacin kuma Kano din na yawan kai wa Katsinar harin yaki.
A kuma daidai wannan wakati da aka yi ta samun baki na kwararowa cikin Katsina saboda ta fara bunkasa ta fuskar addinin islama, sai ma wadannan wurare na ganawa da jama’a aka fara maishe su wararen bautar Allah.
Wannan ya sanya ma, bayan wasu shekaru sai aka tada wasu sabbin garuruwa bayan birnin Katsina ya cika da jama’a. Sannan aka kara wasu sarautu, kamar su sarautun Magajiya Maskumi, Magajiya Yaljigari, Uwar Sarki, Iya, da sauran su. Sanna kuma aka kirkiro wasu sarautu na matan sarki, kai har da su sadakoki da sarki kan ajiye irin su: Mai Lalle, Mai mashariya, Maidaki, Maiwurari, da sauran su. Kowace da aikin ta a fada. Misali, Magajiya Yaljigari ita ke da alhakin kai wa Sarki wani sabon labarin abin da ya faru a cikin birni. Saura kuma kowacce da aikin ta na sha’anin assasa bori da tsafi ko aiki da iskokai. Daga nan sai kuma aka kirkiro wasu sabbin sarautu, kamar su Baraya, Turaki, Jakadiya, Shantali, Ajiya wadanda masu bai wa sarki shawara da wadanda aka yi wa dandaka da sauran bayi ke rike da su. Aikin su shine kula da harkokin ajiyar kudi da adana kayan baitulmali da kuma kula da wuraren zama don yin shawarwari. Daga nan ne kuma aka samu sarautar Galadima da Sarkin Bai.
Wanda ya gaji Sarki Ali Murabus shi ne Aliyu Karya Giwa, kuma, ko da ya ke matashi ne bay a da yawan shekaru, amma duk da haka sai da ya kai harin yaki Yawuri, wadda ke kudu da Sakkwato. Ko da ya ke babu zancen wannan yakin a rubuce, amma tun a lokacin Katsinawa ke tafiya can wajen domin fatauci. Saboda girman kasar Katsina tattalin arzikin ta da karfin dakarun yakin ta su ka karu. Kuma ba mamaki da tun a lokacin Aliyu Karya Giwa aka samu Alkali a birnin Katsina, mai suna Muhammad bin Ahmad bin Abi Muhammad Al Tazakhti. Wannan bawan Allah ya rasu cikin shekara ta 1529 ko 1530 anan birnin Katsina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!