Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Mutum A Kotu Bisa Banka Wa Wata Mata Wuta

Published

on

A ranar Juma’a ne a ka gurfanar da wani mutum mai suna Gerald Edem dan shekara 40 da haihuwa a gaban kotun Ebute Meta da ke Jihar Legas bisa zargin sa da banka wa wata mata wuta. Edem ya gurfana a gaban alkali mai shari’a Tolu Agbona bisa tuhumar sa da laifin kona matar.
Wanda a ke zargin ya musanta laifin da a ke tuhumar sa da shi.
Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, Sufeta D. Raphael, ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifi ne a ranar 28 ga watan Afrilun da misalin karfe 7.50 na yamma a gida mai lamba uku da ke kan titin Auntu Kemi cikin yankin Aga-Ikorodu. Raphael ya na zargin wanda a ke tuhuma da watsa wa Glady Chuk kalanzir tare da banka mata wuta wanda ya yi sanadiyyar konewar jikinta. Ya ce, wannan laifi ne wanda ya sabawa sashi na 245 na dokar kundin tsarin mulkin Jihar Legas ta shekara 2015.
Agbona ya bayar da belin wanda a ke zargi a kan kudi naira 100,000 tare da mutum biyu masu tsaya masa. Ya bayyana cewa, masu tsaya masa ya kansance su na da takardar sheda ta biyar harajin gwamnatin Jihar Legas har na tsawan shekaru uku. Ya kuma dage sauraran wannan kara har sai zuwa ranar 11 ga watan Yuni.
An Cafke ‘Yan Kungiyar Asiri Guda Hudu A Jihar Edo
Rundunar ‘yan sandar Jihar Edo, ta samu nasarar cafke mutum hudu wadanda a ke kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar DSP Chidi Nwabuzor, shi ya bayyana hakan a ranar Asabar. Ya bayyana cewa, wadanda a ke zargin tawagar masu garkuwa da mutane ne, ‘yan fashi da makami, sannan kuma ‘ya’yan kungiyar asiri ne wadanda su ka addabi jihar.
A cikin bayanin nasa, ya bayyana cewa jami’an tsaro na hadin giwa wadanda su ka hada da jami’an tsaro na farin kaya da kuma rundunar ‘yan sanda ne su ka samu nasarar cafke wadanda a ke zargin. Ya ce, “bayan da jami’an tsaron hadin giwa wadanda su ka hada da jami’an tsaro na farin kaya da kuma rundunar ‘yan sanda su ka samu labarin farmakin da su ka kai a Jihar, sai tawagar su ka dauki matakin dakile lamarin. “Kwamishinan ‘yan sandar Jihar Edo, Dan-Mallam Mohammed, ya bayar da umurnin a hada tawar ‘yan sanda wadanda za su dakile ayyukan ta’addanci a Jihar.
“An gudanar da farmaki tare da bincike a yankin Auchi, wanda ya yi sanadiyyar samun nasarar cafke Salihu Uzobehe dan shekara 23, Hadi Musa Gambari dan shekara 23, Tijani Garuba dan shekara 24 da kuma Mohammed Abdulkadri mai shekaru 44 da haihuwa, wadanda su dai kasurguman masu garkuwa da mutane ne da kuma fashi da makami wadanda su ka addabi Jihar Edo da kewaye.”
Abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda a ke zargin dai sun hada da, mota kirar ‘Toyota Balet’, mai lamba kamar haka AG-721-AGZ, bindiga mai sarrafa kanta guda daya, bindiga kirar gida guda biyu, gatari guda 20, inifam din ‘yan sandar mobayal, abun rufe fuska guda biyu da kuma layoyi. “Rundunar tana bukatar mutane da su kai duk wani motsin da ba su aminta da shi ba a wurin ‘yan sanda,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: