Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Gabadaya Iyali Sun Mutu A Cikin Gida A Jihar Legas

Published

on

Mazauya yankin Aga da ke Ikorodu a Jihar Legas, sun shiga cikin firgici lokacin da su ka tsinci gawar uba, mahaifiya da kuma ‘ya’yansu sun mutu a cikin gida ranar Juma’a. Kamfanin dillanin labarai na Nijeriya, wat NAN, ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a gida mai lamba 12 da ke kan titin Obafemi Erija Borokini cikin yankin Age a Ikorodu da misalin karfe 6.30 na safe.
Wani makwabcin mariyayen mai suna Mista Taiwo Salami, ya bayyana wa NAN cewa, an tsinci gawar Mista Charles Omomo wanda a ke yi wa lakabi da Baba Efe tare da matarsa Faith Omomo da kuma yaransu guda uku a cikin gidan su. “Na bar gida tun da sassafe a kan babur dina. Bayan wasu awanni, sai matana ta kira ni a wayar salula cewa, an tsinci gawar Baba Efe tare da matarsa da kuma karamin ‘yarsu mai suna Glorious a cikin gidansu.
“Yana zuwa gida, sai na fara jin ihu a cikin gidan. Na shiga cikin gidan su Baba Efe, san na tarar ya kashe kansa, ga matarsa kwance cikin jini ita ma ta mutu da kuma karamar diyarsu duk sun mutu. “Na yi matukar mamaki, domin a daran jiya na ga matar da kuma mijin ba tare da nuna wani alamar komi ba. Na ma gan su suna wasa da ‘ya’yansu ne. “Ban san abinda ya yi sanadiyyar wannan lamari ba,” in ji Salami.
Ya cigaba da cewa, duka yaran suna tare da iyayansu lokacin da lamarin ya faru. “Yayan Efe ne ya fara fada wa wani daga cikin iyalansu wadanda ke zaune kusa da gidansu faruwar lamarin. Inda ya ke ta ihun neman taimako. “Shi dai wanda ya mutu dan acaba ne, amma a watan da ta gabata ya daina aiki domin babur dinsa ya samu matsala. Haka ma yaransa sun daina zuwa makaranta, na gan su a jiya amma ban ga wata alama ba,” in ji Salami.
Wani makwabcin wanda ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa, Omomo shi da matarsa sun samu rashin jituwa a kwanan nan. “Akwai lokacin da su ka yi rikici har mijin ya na zargin matar a kan ta nuna masa ainihin yaransa, idan kuma ta ki to babu wanda zai rayu a cikinsu. “Kamar yadda ku ke gani a yanzu, ma’auratan su na tare lokacin da lamarin ya faru, sannan babu wani abinda ya samu sauran manyan yaran guda biyu. “An gano gawar matar da kuma yaran a hade, yayin da aka gano cewa, uban ya kashe kansa ne,” in ji makwabcin.
Lokacin da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ziyarci wurin, ya samu ‘yan sanda daga Ikeja da Ikorodu suna kwahe gawarwakina cikin gidan.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda Jihar Legas, DSP Bala Elkana, bai yi wani karin bayani ba a kan lamarin ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!